Jihar Katsina Ma Za Ta Yi Wa Malamanta Jarabawa

0
856
Mustapha Imrana Abdullahi Da Rabo Haladu, Daga Kaduna
KAMAR yadda bayanai suka bayyana cewa kwamishiniyar kula da harkokin ilimi ta Jihar Katsina Furofesa Hakika Sadiyya na cewa tana goyon bayan a yi wa malaman makaranta jarabawa kamar yadda Kaduna ta gudanar.
Kamar yadda ta bayyana cewa a matsayinta na kwamishiniyar ilimi ta samu darasi kwarai musamman daga tattaunawar da ta yi da malamai musamman na kananan hukumomi, wannan ya sa hakika na ga cewa yi wa malaman makaranta jarabawa ya zama wajibi a jihar.
\”Ni a gaskiya, zai yi wa malaman makaranta jarabawa a Jihar Katsina.tuni har na gabatar da batun ga majalisar zartarwar jihar na a gudanar da jarabawar .
Na bayyana bukatar cewa ma\’aikatar ilimi ta jiha ta gudanar da aikin tantance malamai domin mu samu ingantattun malamai a duk fadin jihar baki daya.
\”Kwanan nan bayan mun gudanar da abin da muke kira jarabawar cike gurbi domin cike gurbin malaman da suka mutu ko ritayar aiki, a cikin akalla malamai dubu 12 da suka dauki jarabawar dubu 3, da dari uku ne suka samu maki 35 cikin sittin. Don haka ya zama wajibi a duba halin da ilimi yake ciki a Jihar Katsina.
Saboda haka ina mai bayar da cikakken harin kai da goyon baya a gudanar da wannan jarabawa ga malaman makaranta.
\”Kamar yadda alkalumma suka nuna kuma aka gabatarwa ma\’aikatar ilimi a tun shekarar 2016 akwai malamai 26, ,201 da suka hadar da maza dubu 20,520 mata kuma dubu 5,681.
Kamar dai yadda muka kawo maku rahoto a kwanan baya cewa shugaban hukumar kula da ilimin Firamare na Jihar Kaduna Malam Nasiru Umar Rigachikun ya bayyana cewa akwai akalla jihohi biyar daga arewacin kasar da suka bayyana sha\’awarsu ta yi wa malaman makaranta jarabawa inda ya ce tuni har Jihar Kogi ta zo Kaduna tare da mukarraban gwamnatin jihar sun kuma tattauna domin sanin yadda suka yi wannan jarabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here