PDP Ta Kara Wa’adi Ga Masu Son Tsayawa Takara

    0
    754

    Rabo Haladu Daga Kaduna

    JAM\’IYYAR PDP da ke adawa a Nijeriya, ta tsawaita wa’adin da ta bai wa wadanda ke son tsayawa takarar wasu
    mukamai a babban taronta domin sayen fom daga 19 har zuwa 30 gawannan watan nuwamba.
    Kwamitin da aka dora wa alhakin shirya babban taron zaben sabbin shugabanni, ya ce ya yanke shawarar
    tsawaita wa’adin ne lura da yadda ake samun karuwar jama’a da ke neman tsayawa takarar mukamai.
    Wannan ne dai karo na farko da jam’iyyar ke shirin zaben sabbin shugabanni tun bayan gudanar da zaben shugabancin kasa a Nijeriya inda PDP ta sha kaye.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here