Isah Ahmed, Jos
HAFIZIN ALKUR\’ANI, Tanim A. Yari daga jihar Neja ne ya lashe gwarzon shekara na gasar karatun Alkura’ani mai girma na kasa, karo na 21 da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa ta shirya a birnin Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa, a makon da ya gabata.
A yayin da Mas’ud Idris Gital daga jihar Bauci ya zo na biyu, Misbahu Abubakar daga jihar Kebbi ya zo na uku, Muhammad Auwal daga jihar Gombe ya zo na hudu, Nuhu Adam Ibrahim daga jihar Kaduna ya zo na biyar.
Da yake jawabi a wajen rufe gasar, shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa a duk inda katarun Alkura’ani ya sauka, alheri ya sauka a wajen. Ya ce don haka kungiyar ta tashi tsaye wajen karantar da Alkura’ani a kowanne lungu da sako na Nijeriya da kasashen waje.
Ya ce karatun Alkurani yana bude wa dan’adam basira, don haka ya yi kira ga al’ummar musulmi su rika karatun Alkura’ani saboda alherin da ke tattare da yin haka.
Har’ila yau ya yi kira ga al’ummar musulmi su tashi tsaye wajen koyan harshen Larabci domin su fahimci karatun Alkura’ani. Ya ce babu harshen da ya kai harshen Larabci fusaha da cikakken bayani, kamar harshen Larabci.
Daga nan ya yaba wa Gwamnan jihar Adamawa kan irin goyan baya da tallafin da ya bayar wajen gudanar da wannan gasar karatun Alkura’ani.
A wajen rufe wannan gasa dai, an raba kyaututtukan motoci da baburan hawa da akwatunan talbijin da kudade ga wadanda suka zamo zakaru a gasar.