JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
SAMAR da injunan sarrafa kayan amfanin gona ga manoma da masu kananan masana\’antu zai magance yawan asarar amfanin gonar da manoma ke samu a kowane irin yanayi.
Wannan tsokaci ya fito ne daga shugaban kamfanin samar da injunan sarrafa amfanin gona na \”Shugaban Matasa Nigeria Limited\” da ke Kano, Alhaji Zakari Tijjani Fagge a wata hira da suka yi da wakilin mu, inda kuma ya bayyana cewa yanzu zamani ya canza don haka yana da kyau a fara amfani da injunan zamani wajen sarrafa kayan amfanin gona don inganta su.
Sannan ya sanar da cewa ana yin asarar kayan amfanin gona duk shekara saboda rashin gyara su kamar yadda ake gani a kasashen duniya, don haka ya yi albishir cewa kamfanin sa na Shugaban matasa Nigeria limited dake lamba 19 kan titin Galadima yana da injuna iri-iri kuma na zamani wadanda suke aikin sarrafa kayan amfanin gona cikin hanzari da kuma biyan bukata.
Alhaji Zakari Tijjani Fagge ya kuma bayyana cewa yanzu haka akwai jihohi masu yawa da suke sayen injunan sarrafa kayan amfanin gona a wannan kamfani nasu kuma suke rabawa manoma wanda hakan ya sanya ake gyara amfanin gona cikin sauri tamkar a kasashen waje, sannan ya jaddada cewa za su ci gaba da samar da ingantattun injuna domin amfanin manoman wannan kasa da yardar Allah.
A karahe ya yi bayanin cewa kofar su a bude take ga masu sayen kowane irin nau\’i na injuna walau a gwamnatance ko kungiyoyin manoma ko kuma masu manyan gonaki domin su duba irin injunan da suke kawowa daga kasashen duniya daban-daban.