AN BUKACI GWAMNATIN JIHAR KANO DA TA FARA GYARA KANANAN DAM-DAM DAM A JIHAR-MANOMAN RANI.

0
616
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta fara gyara kananan Dam-Dam da ake da su a fadin jihar domin bunkasa noman rani da samar da abinci da kuma kyautata zamantakewar al\’ummar da ke yankunan karkara.
Wannan sako ya fito ne daga wasu manoma da ke jihar yayin wata ganawa da  suka yi da wakilinmu, inda suka bayyana cewa akwai Dam-Dam masu tarin yawa da suka lalace a gurare daban-daban a jihar,  amma kuma tun lokaci mai tsawo ba a sake waiwayar su ba duk da cewa suna da  matukar amfani ga rayuwar al\’umma.
Sannan sun sanar da cewa yanzu noma da kiwo su ne kashin bayan ci gaba a mafiya yawan kasashen da suka ci gaba a fadin duniya, don haka yana da kyau gwamnatin Jihar Kano bisa jagorancin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta fara gyaran kananan Dam-Dam da suka lalace sakamakon ballewar da ruwa ya yi ba ya zama tun da dadewa.
Malam Sulaiman Waddau daga yankin karamar hukumar Dawakin Tofa ya nunar da cewa akwai wani Dam wanda aka haka tun kimanin shekaru fiye da arba\’in ana amfani da shi a garin Kunnawa, amma yanzu haka ya karye ruwa ba ya zama tun kimanin shekaru biyar amma bai sami kulawar gwamnatin jiha ba ko kuma ta karamar hukumar Dawakin Tofa wanda hakan abin a duba ne.
Shi ma wani manoni da ke yankin karamar hukumar Tofa Alhaji Musa  Bello ya bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta gyara wasu daga cikin Dam-Dam din da suka lalace  ta yadda manoman yankin zasu ci gaba da sana\’ar su ta noman rani kamar yadda ake yi a sauran manyan Dam-Dam din da  domin kara inganta rayuwar mazauna kusa da wadannan gurare rani da damina.
Daga karshe manoman sun nuna gamsuwar  su bisa yadda gwamnatin Jihar Kano take aiwatar da manufofinta  a fannin aikin noma domin samar da abinci da ayyukan dogaro dakai batare da nuna gajiyawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here