JAMI\’AN HUKUMAR KIYAYE HADURRA SHIYYAR DAMBATTA SUN SAMI YABO DAGA DIREBOBI.

0
682
Jabiru A Hassan,Daga Kano.
DIREBOBI da sauran masu ababen hawa da ke aiki kan hanyar Kano zuwa Daura sun nuna gamsuwar su bisa yadda jami\’an hukumar kiyaye hadurra shiyyar Dambatta suke gudanar da ayyukansu a wannan hanya ba tare da nuna gajiyawa ba.
Sannan sun nunar da cewa  ana samun fahimtar juna tsakanin jami\’an na FRSC da kuma direbobin motoci musamman dangane da bin ka\’idojin hanya da sabunta takardun ababen hawa da yin tuki cikin natsuwa da rage mugun lodi da kuma kula da lafiyar ababen hawa.
Amadu Sani, wani direban motar fasinja da ke yin jigila kan wannan hanya ta Dambatta,  ya bayyana wa wakilinmu cewa yadda jami\’an hukumar FRSC shiyyar Dambatta suke gudanar da aikinsu ya taimaka wajen rage aukuwar munanan hadurra kan wannan hanya, sannan suna wayar da kawunan direbobi da sauran masu ababen hawa kan tuki cikin natsuwa da kuma nuna illolin yin mugun lodi domin samun kudi wanda ta haka ne ake samun hadurra masu muni.
Haka kuma mafiya yawan direbobin da wakilin namu ya zanta da su sun bukaci \’yan uwansu direbobi dama sauran masu kananan ababen hawa da su tabbatar suna bin ka\’idojin tuki domin kauce wa aukuwar hadurra, tare da jaddada cewa za su ci gaba da baiwa jami\’an hukumar ta FRSC hadin kai wajen gudanar da ayyukansu domin a hada hannu wajen rage hadurra a kan tituna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here