Ko Da Buhari Zai Yi Magudi A Zaben 2019 Ba Zai Ci Ba…. Inji Balarabe Musa

    0
    712

    Rabo Haladu Daga Kaduna

    TSOHON Gwamnan jihar Kaduna kuma shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa koda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aringizon kuri’u a zaben 2019, hakan ba zai hana shi faduwa zabe ba, saboda ba ma ‘yan jam’iyyar adawa ba, magoya bayansa ma sun cire tsammani daga gare shi.
    “Idan har Buhahri yana tunanin yana da farin jini har yanzu kamar yadda yake da shi kafin ya ci zaben 2015, to ya yaudari kansa”
    Ya ci gaba da cewa” Domin ya sabawa wadanda suka zabe shi saboda ya jefa su cikin kuncin rayuwa. Domin tun daga lokacin da ya hau mulki kasar take ta fadawa matsaloli daban- daban” inji shi

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here