EFCC Ta Tsare Anyim Pius Anyim Wata Daya

0
761

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

TSOHON sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya Anyim Pius ana zarginsa ne da matsalar bayar da kwangilar da kudin ta ya kai Biliyan 13 ga wasu kamfanoni da yake da danganta ka da su, kuma ya karbo Miliyan dari biyar da ashirin daga hannun Sambo Dasuki.
Rahotanni sun bayyana cewa \” Gaskiya ne mun samu takardar izini daga kotu a kan yadda za mu ci gaba da tsare shi har na tsawon wata daya wato kwanaki talatin kenan daidai, kamar yadda EFCC ta ce wannan zai taimaka masu domin samun sukunin gudanar da bincikesu.\”
Majiyarmu ta ci gaba da cewa Anyim ya zama sakataren gwamnatin tarayya daga watan Mayu 2011 zuwa watan Mayu 29, 2015, kuma asusun ajiyarsa da babban bankin Nijeriya ya karbi kudi Naira 58,146,983,677.85.
\”Daga wannan asusun guda uku suna da dangantaka da shi Anyim kai tsaye tsawon shekaru kuma su ne Obis Associate da Eldyke sun karbi kwangilar sama da Biliyan 13 kuma an karbi kudi Miliyan 10,308,017, 838.85 tsakanin 2014 zuwa 2015.
A wajen karantarwa kudin kamfanin Fandusho da Br Kthru sun aike da kudi ga wurare 37 wasu daga cikin wadanda suka karbi kudin ba su da wani alama da batun aikin zaizayar kasa.
A watan Maris 2017 kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin babban birnin tarayya Abuja ya yi kiran a hukunta tsohon sakataren gwamnatin tare da Bala Mohammed tsohon ministan Abuja, duk a kan batun gina sabon birnin a garin na Abuja.
In dai za a iya tunawa aikin gina sabon birnin aiki ne da gwamnatin Jonathan ta kirkiro da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here