GWAMNATIN YOBE TA RABA FILAYEN GINI KIMANIN 307 GA WASU \’YAN GUDIN HIJIRAR KUKARETA

0
725
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GWAMNATIN Jihar Yobe ta rarraba fulotai, wato filayen gina gidaje kimanin 307 hade da kayayyakin ginin da kudadensu ya kai kusan Naira Dubu 30 ga wasu \’yan gudun hijira da ke sansaninsu a kauyen Kukareta cikin karamar hukumar Damaturu don wadannan mutane su samu damar gina gidajensu.
Gwamnan jihar ne Alhaji Ibrahhm Gaidam wanda mataimakinsa Injiya Abubakar D. Aliyu ya wakilta, ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da  ba da kayayyakin tallafin ginin ga \’yan gudin hijirar a kauyen na Kukareta, yadda ya ci gaba da cewa wannan tallafi da aka bai wa wadannan \’yan gudun hijira su ci gaba da rayuwa a wurin da suke a yanzu ganin cewar mafi yawansu sun zabi hakan duk da cewar ba daga wuri guda suka fito ba, wasunsu daga makwabciyar jihar suke wato jihar Borno.
Gwamnan ya ba su tabbacin cewar, gwamnatinsa za kuma ta samar musu da kayayyakin kula da lafiyarsu wato gina asibiti da kuma samar musu makarantu don bada dama  ga yaransu su samu ilimi mai inganci da sauran abubuwan more rayuwa.
Da yake jawabin a wajen wannan biki shugaban majalisar karamar hukumar Damaturu Alhaji Bulama Madu yabawa ya yi ga gwamna Ibrahim Gaidam dangane da irin yadda yake nuna damuwarsa ga kula da rayuwar \’yan gudin hijirar.
Kayayyakin ginin da aka bayar tallafi ga \’yan gudin hijirar sun hada da Fuloti 307 masu kimanin tsawon 100/50 da kuma kwanukan rufi da katakai da siminti da kudadensu ya kai Naira Miliyan 9 da dubu dari 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here