KAFA DOKAR HANA KIWO ZAI KAWO MATSALA A NIJERIYA-SALE BAYARE  

  0
  789

  Isah Ahmed, Jos 

  Alhaji Sale Bayare shi ne sakataren kungiyar ci gaban al’ummar Fulani ta Nijeriya ta Gan Allah. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan kafa dokar hana kiwo da jihohin Ekiti da Bemuwai suka yi, ya bayyana cewa kafa wannan doka zai kawo matsala a Nijeriya. Ga tadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; Mene ne za ka ce dangane da yadda jihohin Ekiti da Benuwai suka kafa dokar hana kiwo, kuma jihar Taraba ma tana nan tana kokarin kafa wannan doka?

  Sale Bayare; Wato wadannan abubuwa da suke faruwa na kafa wannan doka ta hana kiwo, wasu abubuwa ne na bakin ciki. Wannan sana’a ta kiwo da makiyaya suke yi, ba dokar Nijeriya ce ta haramta ta ba. Saboda kowanne dan Nijeriya yana da ‘yan cin ya yi walwala kuma ya nemi abin da zai ci a Nijeriya. Saboda haka muna mamaki yadda aka fara kafa wannan doka kamar da wasa a jihar Ekiti.

   Yanzu kuma ga jihar Benuwai itama ta kafa wannan doka.

  Ita ma jihar Taraba tana nan tana maganar cewa wannan doka za ta fara aiki a jihar a watan janairu na sabuwar shekara mai zuwa.

  Muna ganin wannan abu wani karamin wuta ne da ya taso wadda idan ba a yi hankali ba za ta ci Nijeriya baki daya. Saboda a ce makiyaya wadanda sun kai sama da mutum miliyan 20  an hana su harkar kiwo a Nijeriya. Kuma ana yin misalai da wasu kasashe da suka ci gaba na Turai. Muna son mu gaya wa duniya cewa wadannan kasashe da suka ci gaba ba su da makiyaya na gargajiya. Don haka ba sa yin kiwo na gargajiya. Suna yin kiwo na zamani ne.

  Mu kuma makiyayanmu a nan Nijeriya da kasashen Afrika tun lokacin da Annabi Musa ya fara kiwo har ya zuwa yau, makiyayanmu suna tashi daga wannan waje suna bin ciyawa da ruwa idan ruwan ya yi yawa su tashi su koma can. Don haka makiyayanmu har sukan tafi yankunan Yarbawa da Iyamurai da Neja Delta su zauna. Saboda Nijeriya kasa ce da kowanne dan Nijeriya yake da \’yancin ya je ya zauna a duk inda ya ga dama. Saboda haka wannan mataki da wasu jihohin Nijeriya suka fara dauka na kafa dokar hana kiwo a jihohinsu yana ba mu mamaki kwarai da gaske.

  Wannan ruwa na kogin Benuwai ba na jihar Taraba ko Benuwai ba ne. Wannan ruwan kogi ruwa ne daga Allah, wadda ya taso tun daga kasashen Kamaru ya gangaro ta duwatsun Mambila har zuwa teku da ke Legas. Saboda haka babu wani mutum da zai ce albarkatun ciyawa da ruwa da ke wadannan wurare na wani ne. Saboda haka muna gaya wa gwamnatin jihar Benuwai cewa wannan doka da suka kafa ya kamata a sake duba ta. Saboda mun fahimci cewa a cikin wannan doka, akwai tozartawa da kabilanci da banbancin addini da cin mutuncin makiyaya. Mun fahimci cewa an kafa wannan doka ne domin a musguna wa mutanenmu. Saboda kabilancin kabila da addini da kiyayya da hassadar da ake yi wa mutanenmu. Saboda haka muna kira ga Gwamnan jihar Benuwai ya dubi matsalar da ke tattare da wannan doka.

  Shi kuma Gwamnan jihar Taraba muna son ya sani cewa doka ce ta kafa ofishin Gwamna kuma doka ce ta ba shi ayyukan da yake yi.

  Bayan faruwar rikicin yankin Mambila da aka yi a kwanakin baya, mun bi dukkan matakan da suka kama a dauka mun dauka. Mun bai wa mutanenmu hakuri kan kisan gillar da aka yi wa mutanenmu daga nan muka dauki mataki na kai gwamnatin jihar a gaban babbar kotun jihar, muka yi karar gwamnan kan cewa bashi da hurumin kafa wannan doka  a kundin tsarin mulkin Nijeriya na kafa dokar hana kiwo a jihar.   Bayan haka mun sake kai karar gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya a gaban kotun Afrika ta yamma kan wannan kafa doka ta hana kiwo a jihar Taraba da kuma abin da aka yi wa mutanenmu yankin Mambila da ke wannan jiha. Haka kuma mun sake kai karar gwamnatin jihar ta Taraba da gwamnatin tarayya a gaban kotun duniya kan kisan gillar da aka yi wa mutanenmu a wannan jiha. Don haka ba mu ga dalilin da zai sanya gwamnan jihar Taraba ya dauki doka a hanunsa ya kafa wannan doka ba, domin mun kai kara gaban kotuna har guda uku kan wannan al’amari.

  GTK; Wadanne irin illoli ne kake ganin kafa wannan doka zai kawo a Nijeriya?

  Sale Bayare; Kamar yadda muke gaya wa mutane lokacin da aka fara kafa wannan doka a jihar Ekiti muka ce idan ba a yi wani abu a kan wannan al’amari ba. Wata jiha ma za ta ce za ta yi, domin akwai jihohi da yawa da suke gaba da makiyaya domin an dauko addini da kabilanci a sanya a maganar makiyaya a Nijeriya. Amma abin bakin ciki gwamnatocin Nijeriya ba su iya yin komai ba kan wadannan abubuwa da ake yi wa makiyaya.

  Idan kace za ka kori makiyaya a duk wuraren da suke da ciyawa da ruwa. Jihar Nasarawa ba za ta iya daukarsu ba. Jihar Neja ba za ta iya daukarsu ba, jihar Kwara ba za ta iya daukarsu ba, jihar Kogi ba za ta iya daukarsu ba, jihar Filato ba za ta iya daukarsu ba, jihar Bauchi ba za ta iya daukarsu ba, Jigawa ko Barno ba za su iya daukarsu ba. Abin da muke fada shi ne a yi mana adalci. Matsalar wannan doka  a fili take.

  Mu ba mu da wata sana’a sai wannan sana’a ta  kiwo, ita ce iyayenmu da kakanninmu suka yi, da ita muke ci da ita muke sha, don haka  duk wanda ya hana mu wannan sana’a ya tsokano bala’i.

  GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati dangane da hanyoyin da za a bi, a warware wannan matsala?

  Sale Bayare; Abin da muke so gwamnatin tarayya tayi shi ne muna son a fitar da Fulani makiyaya daga ma’aikatar gona ta tarayya. Domin wannan ma’aikata masifa ce a wurin Fulani makiyaya. Saboda an ce wannan ma’aikata ce ta manoma da Fulani makiyaya amma yanzu wannan ma’aikata ta zama ma’aikatar manoma kadai.

  Mu abin da muka sani kasar nan mu ne miya manoma ne tuwo, kaga idan babu miya babu yadda za a ci tuwo. Saboda haka ya kamata a yi mana adalci a wannan ma’aikata ta hanyar ware mana kasonmu a duk kasafin kudin da za a yi.

  Don  haka muna son gwamnatin tarayya ta tsaya wajen ganin an yi mana hukumar kula da makiyayan Nijeriya. Wadda za ta kula da harkokin kiwo a Nijeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here