MASU KANANAN SANA\’O\’I  SUN GAMSU DA TSARIN  BICHI MICROFINANCE BANK

  0
  948
  Jabiru A Hassan,Daga kano.
  MASU hulda da bankin ba da rance na Bichi sun nuna gamsuwar su bisa yadda bankin yake kara bullo da hanyoyin tallafa masu ta yadda sana\’o insu za su bunkasa ta kowane fanni.
  Sannan sun sanar da cewa yanzu al\’ummar wannan yanki sun fahimci cewa bankunan ba da rance ga masu kananan sana\’o\’i su ne cibiyoyin kudi mafi kusanci da su idan aka dubi yadda suke taimaka wa \’yan kasuwa da masu kananan masana\’antu ba tare da nuna gajiyawa ba.
  Haka kuma mafiya yawan muyanen da wakilin mu ya gana da su sun sanar da cewa bankin yana kokari kwarai da gaske wajen ganin masu kananan sana\’o\’i suna samun kulawa ta musamman domin cimma manufofin kakkafa ire-iren wadannan bankuna ganin yadda ake da kwararrun ma\’aikata kuma marasa kyamar jama\’a a wannan guri.
  Bugu da kari, wasu mata da aka tattauna da su sun bayyana cewa bankin ba da rance ga masu kananan sana\’o\’i na Bichi yana bai wa mata kulawa ta musamman domin su kara bunkasa sana\’o\’in da suke yi, tare da yin kira ga dukkanin wadanda suke karbar rancen kudi don yin sana\’o\’i su rika biyan bashin ta yadda za a sami damar bai wa wasu domin su ma su amfana da wannan abin alheri.
  Daga karshe, dukkanin mutanen da suka yi bayanai sun yaba wa shugabannin wannan banki saboda kyautata wa mutane da suke yi a duk lokacin da suka je banki bisa wani al\’amari da ya shafi sha\’anin kudi ko kuma shawarwari kan fara sana\’a.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here