Ta Shirya Bita Kan Tarbiyyar \’Ya\’ya Mata

0
864

Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
KUNGIYAR \’yan uwa mata musulmi (MSO) ta kasa reshen Jihar Yobe ta shirya taron bita na kwana guda ga mata matasa kimanin 50 kan abin da ya shafi tarbiyya a matsayinsu na iyaye.
Wannan taron bita dai an gudanar da shi ne a babban masallacin jumu\’a da ke cibiyar kula da addinin musulunci da ke garin Damaturu wadda ya samu halartar mambobin kungiyar da ma mambobin kungiyoyin addinin daga
kowane bangaren Jihar ta Yobe.
Da take jawabi ya yin bikin bude wannan bita Amira ta kasa ta wannan kungiyar MSO wacce Hajiya  Jummai Baba Dauda ta wakilta ta yaba wa wannan kungiya a matakin Jihar ta Yobe dangane yunkurin gudanar da wannan taron bita da ta yi.
Shugabar ta kara da cewar a matsayin mata iyayen al\’umma wannan kudiri kan abin da ya shafi kula da tarbiyya da ta shirya abin a yaba ne musamman dangane da \’ya\’ya mata suka samu kan su ciki wadda tabarbarewar tarbiyya shi ya haifar.
Malamai da dama sun gabatar da madaloli a wajen wannan taro na bita da suka hada da Malama Hauwa Idris da Rukayya Salisu da kuma Malam Abdulrahman Khamis musamman kan abin da ya shafi rainon yara da suturun \’ya\’ya mata da sauran fannoni na tarbiya hade kuma da irin rawar da kafofin sadarwa na zamani ke takawa kan gurbata tarbiya ga \’ya\’ya mata da ma matasa baki daya.
A jawabinta na maraba da baki Amirar kungiyar MSO a Jihar ta Yobe Hajiya Magajiya Mohammf Kellumi ta ce kungiyarsu ta yi yunkurin gudanar da wannan bita ne don jaddada muhimmancin da \’ya\’ya mata ke da su cikin al\’umma.
Don haka ta kirayi \’yan uwanta mata da kuma iyaye maza da su ci gaba da sa hannun wajen ba da tarbiyya ta gari ga \’ya\’ya mata da ma dukannin matasa.ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here