Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTANNI daga jihar Katsina sun ruwaito cewa an tsinci gawar sakataran jam’iyyar APC na karamar
hukumar Dutsin-ma Alhaji Idris Bature a mace .
Kwamishinan \’yan sandan jihar Katsina, Besen Gwana shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.
Duk da dai bai yi wani karin haske a kan yadda mutuwar take ba. Kwamishinan \’yan sandan ya kuma bayyana cewa Bala Idirs, wanda ake wa lakabi da Ubangaja ,bisa zarginsa da hannu wajen mutuwar mamacin
Kwamishinan ya ce wanda ake zargin Ubangaja mai shekaru 53 wanda suke unguwa daya da mamacin, a ranar
19/11/2017 da misalin karfe 20:30 ya nemi shi mamacin da ya raka shi zuwa kauyen Kuki da ke cikin karamar
hukumar Dutsin-ma, sai dai kawai aka tsinci gawar mamacin duk an ji masa raunuka a jikinsa.