Atiku Abubakar Ya Fice Daga Jam\’iyyar APC

  0
  696

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  TSOHON mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam\’iyya
  mai mulki ta APC.
  Shugaban kungiyoyin da ke goyon bayan Atiku Abubakar ya tabbatar wa da manema labarai  wannan labari,
  sai dai bai bayyana jam\’iyyar da yake son komawa ba zuwa yanzu.
  A wata sanarwa da Atikun ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam\’iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukar wa \’yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki.
  Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman- zamansa jagororin jam\’iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam\’iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam\’iyyarsa ta PDP.
  Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.
  \”A kan wannan dalili ne mambobin jam\’iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin binkundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci.\” Atiku \’na so talakawa su karbi mulki\’ \”A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam\’iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam\’iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni,\” a cewar sanarwar.
  Sanarwar ta ci gaba da cewa: \”Duk jam\’iyyar da ba za ta kula da al\’amuran matasa ba to matacciyar jam\’iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne.\”
  A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam\’iyya daga waccar zuwa wata.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here