Rabo Haladu Daga Kaduna
BABBAN sakataren kungiyar Jama\’atu Izalatul Bid\’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta cewa yana yawan ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin wa\’azinsa.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa manema labarai ya ce shi a tarihin rayuwarsa bai taba ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba a cikin wa\’azinsa.
Malamin addinin ya ce, \”idan akwai wanda ke da wani kaset na wa\’azinsa da ya ambaci sunan malamin, to kofa a bude take ya fiddo da shi ya yada wa duniya.\” cikin wa\’azinsa, domin ya kira sunana da na mahaifina ba sau daya ba, ya kuma kira shugaban kungiyarmu da sunansa karara, har ma yakan siffantashi da munanan siffofi wanda shi
shugaban bai taba mayar masa da martani a kan hakan ba,\” in ji shi.
Jagoran Izalan ya ce \”ita da\’awa ta ahlul sunnah ba da\’awa ce ta kiran sunaye ba.\”