KAMFANIN SHIRYA TAFIYE-TAFIYE NA DALA AIR SERVICES  YA CIMMA NASARA-MATAFIYA.

0
666
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
MASU yin tafiye-tafiye ta hannun  kamfanonin shirya tafiye-tafiye da ke Kano sun nuna jin dadin su bisa yadda kamfanin Dala air services yake kulawa da matafiya daga nan gida Nijeriya har zuwa kasashen duniya da suke zuwa domin harkar kasuwanci ko kuma ibada.
Sannan sun bayyana cewa kamfanin yana kokari wajen kare mutuncin abokan huldar sa da kuma basu kulawa wajen samar da yanayi mai gamsarwa na tafiye-tafiye ba tare da nuna gajiyawa ba, wanda hakan ce ta sanya kowane matafiyi yake kokarin yin hulda da wannan kamfani.
Haka kuma dukkanin mutanen da suka zanta da wakilin mu sun nunar da cewa kamfanin Dala air services yana da ma\’aikata masu amana da sanin ya kamata wadanda kuma suke da kwarewa wajen harkar shirya tafiye-tafiye da kuma kula da matafiya tun daga nan gida Nijeriya har kasashen da suke zuwa domin ganin kowane matafiyi yana jin dadin hulda da kamfanin.
A nasa  bangaren, shugaban kamfanin Alhaji Sa\’idu Ali  ya jaddada cewa kamfanin su zai ci gaba da bullo da kyawawan hanyoyi na bunkasa hulda tsakanin sa da matafiyan dake yin tafiye-tafiye ta hannun su, inda kuma ya sanar da cewa dukkanin masu hulda da su za su ci gaba da  gamsuwa  da tsare-tsaren  da kamfanin ke yi masu cikin yardar Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here