ZABEN 2019: Buhari Sai Ya Riga Rana Faduwa A Jihar Katsina… Sanata Tsauri

  0
  694

  Rabo Haladu Daga  Kaduna

  TSOHON dan majalisar dattawa daga jihar Katsina Sanata Umar Ibrahim Tsauri, ya bayar da tabbacin cewa a
  zaben shekarar 2019 mai zuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai riga rana faduwa a jihar Katsina, inda ya ce gwamnatin Buhari ta APC ta gaza cika alkawuran ‘yan Nijeriya.
  Sanata Umar Ibrahim Tsauri, wanda dan takarar kujerar sakataran jam’iyyar PDP ta kasa ne, ya bayyana cewa a zabe mai zuwa Katsinawa sun shirya yi wa Buhari warwas, yana mai cewa babu wani aikin ci gaba da gwamnatin Buhari ta kawo a jihar Katsina.
  Sanata Tsauri, ya bayyana haka ne a Abuja yayin da  yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sakataran jam’ iyyar PDP na kasa.
  Tsauri ya ce Al’ ummar Nijeriya sun gajji da gwamnatin APC, hasalima, babu wani abin a zo a gani da gwamnatin Buhari ta kawo a cikin shekaru uku da ta yi tana mulkin kasa.
  Ya ce tuni jam’iyyar PDP ta kammala shirinta na amshe mulki daga hannun APC a zaben 2019,inda ya ce shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa na jam’iyyar PDP ne.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here