Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN Muhammadu Buhari, ya rantsar da kwamitin da zai bayar da shawara kan karin albashi mafi karanci ga ma\’aikata.
Wata sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnati ta ambato Shugaba Buhari yana cewa za ta kara albashin bayan shawara da wani kwamiti da aka kafa a shekarar 2016 ya bayar domin gano yadda za a rage radadin tasirin karin kudin mai kan talakawa.
Shugaba Buhari ya ce yana fatan kwamitin, da ya hada da gwamnoni da shugabannin ma\’aikata da sauran masu ruwa da tsaki, zai cimma matsaya kan albashi mafi karanci da ya kamata a biya ma\’akaci a Najeriya. Ana sa ran kwamitin dai zai mika matsayar da ya cimma nan ba da dadewa ba.
A shekara 2016 ne dai aka kara kudin litar mai daga naira 86 zuwa 145 yayin da mafi karancin kudin da ake biyan ma\’aikaci a Najeriya ya tsaya a kan Naira 18,000 kamar yadda yake a da can.
Karin kudin mai ya sa kayayyaki sun kara tsada a kasuwa, kuma kudin shiga na ma\’aikata kuma bai karu ba.