Shugaban kasa Ya Umarci Gwamnoni Su Biya Ma’aikata  Duk Basussukan Albashin Da Suke Bi Kafin Bikin Kirisimeti

0
811

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jihohin kasa a fadarsa da ke Abuja, inda batun basussukan albashin ma’aikata ya mamaye taron.
A lokacin taron shugaba Buhari ya ja kunnen gwamnonin jihohin  da su gaggauta biyan basussukan albashi ga
ma’aikata kafin bikin Krismeti na watan gobe.
Shugaban wanda ya bayar da umarnin biyan kashi 50 daga cikin dari na karshe ga jihohi daga kudaden da aka
dawo da su na Paris Club, ya nuna muhimmancin biyan albashi.
Da yake yiwa manema labarai karin bayani, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce batun ma’aikata ne ya
mamaye taron da suka yi da shugaba Buhari, inda shugaban ya nuna damuwarsa musamman kan ma’aikatan
da suka dogara kan albashi domin su ciyar da iyalansu da biyan kudin haya.
Gwamnonin dai sun tabbatarwa shugaban cewa da zarar sun sami kudaden Paris Club, to kowacce jiha za ta dage ta biya ma’aikatanta albashi.
Sai dai Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Ahmad El-Rufa’I, ya ce ma’aikatan jiharsa ba sa bin gwamnati bashin albashi,amma ya ce wasu jihohin bashin da ake binsu ya fi kudaden Paris Club din da za su samu a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here