Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN jihar Kaduna ta bayyana sallamar ma\’aikatan kananan hukumominta fiye da 4,000 don rage kudaden da take kashewa a matsayin albashi da kuma bunkasa kudaden gudanar da ayyukan raya kasa.
Gwamnatin wadda ta tabbatar da haka a wani taron manema labarai a Kaduna, ta ce matakin ya zama dole don kuwa akasarin ma\’aikatan na karbar albashi ne ba tare da aikin komai ba.
Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Ja\’afaru Sani ya ce gwamnati ta yi wa ma\’aikata 3,159 ritaya, yayin da kuma ta kori wasu 8,083 daga aiki.
Ya ce su kuma za su samu albashin wata daya kuma a ba su garatuti amma ba za a biya su fensho ba.
A cewarsa matakin zai ba wa kananan hukumomin jihar Kaduna damar gudanar da ayyukan raya kasa da kuma biyan albashi ba tare da antallafa musuba matakin ka iya haifar da ce-ce-ku-cen da aka yi a baya sakamakon sanarwar sallamar malaman makarantun firamare sama da 20,000 saboda gaza samun maki 75 a wata jarrabawar
\’yan aji hudu da ta yi musu.
Duk da bayanan da gwamnati ta sha yi kan fa\’idar matakin amma wasu na ganin hakan a matsayin bi-ta-da-kulli ga jama\’a kawai, in ji shi.
Alhaji Ja\’afaru Sani ya ce idan martabar kananan hukumomi ta dawo kuma talaka ya san cewa karamar hukuma tana yi masa aikin da ya dace, shi kansa yadda zai rika hulda da ita zai sauya.