Gobara Ta Kona Dakunan Kwanan Daliban A Nasarawa

0
698

Rabo Haladu Daga Kaduna

WATA gobara da ta tashi a wata Kwalejin Gwamnatin tarayya ta yan mata da ke garin keffi a jihar Nasarawa ta yi sanadiyyar kone biyu daga ciki dakunan kwanan daliban makarantar kurmus.
Rahotanni sun bayyana cewa wutar ta tashi da misalin karfe 7:45 na daren Lahadin da ta gabata, inda ta rika ci har zuwa wayewar garin Litinin, ta kuma kone gine-ginen dakunan kwanan daliban makarantar.
An kuma gano cewa lokacin da wutar ta tashi daliban na dakin cin abinci sai dai litattafai da kayyaykin daliban duka sun kone kurmus ba a samu nasarar fita da komai ba daga yankin da wutar ta tashi.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan wutar ita ce irinta ta farko da ta tashi a makarantar bayan shekaru 18 da samar da makarantar.
Da fari dai an shirya fara gudanar da jarabawar zango na farko a ranar Talatar nan, sai dai sakamakon wannan gobara jarabawar baza ta yiwu ba, inda ake jiran umarni daga ma’aikatar ilimi ta Najeriya don jin sabuwar ranar da hukumar za ta tsayar don fara jarabawar.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here