ZAGON KASA: Majalisar Dokokin jihar Kaduna Ta Dakatar Da Wasu ‘Yan Majalisa 2

0
715

Rabo Haladu Daga Kaduna

RAHOTANNI daga zauren Majalisar dokokin jihar Kadunu Majalisar dokokin jihar Kaduna sun tabbatar da cewa majalisar ta dakatar da wasu ‘yan majalisar guda biyu bisa samun da laifin aikata ba dai dai ba.
\’Yan majalisar da aka dakatar sun fito daga mazabar Zango Kataf da Kaura duk a cikin jihar ta Kaduna.
Rahotanni sun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da \’yan majalisar ta guda biyu daga kudancin Kaduna har sai illa ma sha Allah.
Sai dai har lokacin da muke kammla rubuta wannan rahoton majalisar ba ta yi wani cikakken bayani a kan dakatarwar ba Sai dai rahotanni sun ce dakatarwa tana da nasaba da laifin yi wa majalisar zagon kasa da aka same su da shi.
\’Yan alisar da aka dakatar sune Dakta Bityong Yakubu Nkom, da kuma Honorabul Danladi Angulu Kwasu mai wakiltar
karamar hukumar Kaura dukkansu sun kasance daga kudancin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here