KWADAYIN MULKI NE YAKE SANYA ‘YAN SIYASAR NIJERIYA CANZA SHEKA-FARFESA DADARI

  0
  843

    Isah Ahmed, Jos

  Farfesa Salihu Adamu Dadari malami ne a sashen bincike da nazarin aikin gona na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai shirhi ne kan al’amuran yau da kullum. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa ‘yan siyasar Nijeriya da suke canza sheka daga jam’iyyunsu suna komawa wasu jam’iyyun, masu son mulki ne, ba masu son gyara kasa ba. Har’ila yau ya yi bayani kan yaki da cin hanci a Nijeriya tare da nuna damuwa kan yadda ba a bai wa aikin noma kaso mai yawa ba, a kasafin kudin sabuwar shekara mai zuwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; A ‘yan kwanakin nan wasu ‘yan siyasar Nijeriya suna ta canza sheka daga jam’iyyunsu suna komawa wasu jam’iyyun yaya kake kallon irin wannan al’amari na ‘yan siyasar Nijeriya?

  Farfesa Dadari; Wato siyasar ra’ayi da akida ita ce siyasa ta gaskiya. Amma irin wannan hali na ‘yan siyasar Nijeriya na tsale tsale ko sun sami  mulki ba za su komai na cigaba ba. Saboda suna canza sheka ne  don su sami biyan bukatarsu ta neman mulki. Amma da ana siyasa ne tsakani da Allah, don a yi wa jama’a aiki irin wannan tsale tsale ba zai taso ba. Don haka duk dan siyasar da ka ga yana canza sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan jam’iyya, idan ya sami biyan bukata babu abin da zai yi wa jama’a.

  Saboda idan ‘yan siyasa suna son su yi wa jama’arsu aiki ne to su rika zama a cikin jam’iyyunsu suna yi wa jama’arsu aiki. Kuma ya kamata jama’ar Nijeriya su dauki mataki watsar da  duk  dan siyasar da ya canza sheka ya koma wata jam’iyya. Domin yana neman biyan bukatarsa ne na mulki, ba don ya yi wa jama’a aiki ba.

  GTK; Mene ne za ka ce dangane da shirin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari take yi a halin yanzu?

  Farfesa Dadari; Cin hanci da rashawa a Nijeriya yana da tarihi. Domin tun lokacin da aka karbi mulkin Nijeriya daga hanun turawan mulkin mallaka, shugabannin kasar nan na baya sun yi wa kasar nan adalci. A lokacin babu man fetur amma duk da haka, an yi kokarin yadda kasar za ta ci gaba ba tare da sace-sacen kudaden kasar ba.

  Amma sai aka wayi gari  soja suka karbi mulki suka ji dadi. Kudade suka shiga hannunsu. Har ta kai ga wata gwamnatin soja ta fito ta fadawa duniya cewa matsalar Nijeriya a lokacin, ita ce yadda za ta kashe kudaden Nijeriya, saboda kudade sun yi yawa. Wannan ya sanya ‘yan jari hujja suka hau kan Nijeriya, sai da suka yi daidai da tattalin arzikinta,  suka rika diban kudaden Nijeriya suna kaiwa waje. Suka jefa mu cikin bashi wannan shi ne ya yi sanadin lalacewar Nijeriya.

   A takaice dai mulkin sojoji ne sanadin lalacewar Nijeriya musamman kan cin hanci da rashawa. Domin tun daga lokacin sojoji cin hanci da rashawa ya bunkasa  aka wayi gayi ko aiki za a dauki mutum, dole sai ya bayar da cin hanci. Idan mutum ya mutu yana aiki, idan iyalansa za su karbi hakkokinsa sai sun bayar da cin hanci.

  Za ka ga ma’aikaci yana da gidaje sama da 100 a Abuja, kuma kowa ya san cewa albashinsa bai fi ya gina gida daya ba. Kudaden kasar nan da aka sace aka kai kasashen waje su ne ake zuwa a karbo rance, kuma a zuba mana ruwa. Akwai zaluncin da ya kai wannan?. Sai aka wayi gari Allah ya kawo gwamnatin Buhari ta zo ta kama wannan aiki, na yaki da wannan mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa a kasar nan. 

  GTK; To a ganin ka gwamnatin Buhari ta sami nasarar wannan yaki na cin hanci da rashawa da take yi?

  Farfesa Dadari; Gwamnatin Buhari ta yi kokari wajen fito da tsarin ajiye kudaden gwamnatin tarayya a asusu daya. Domin ta dalilin wannan tsari kudi na zuwa wajen gwamnati  kai tsaye. Amma matsalar da aka samu ita ce shin ana amfani da kudaden da aka kwato? Domin talakan Nijeriya yana cewa har yanzu bai gani a kasa ba. Ita kuma gwamnati tana cewa kudaden da aka karba, sai doka ta bayar da umarnin a yi amfani da su tukuna.

  A gaskiya a tafiyar akwai sanyi domin muna son mu ga an kama ayyuka da wadannan kudade da aka kwato.  Duk da mun san cewa kudaden da aka samu daga mai ba sa isa wajen kasafin kudin kasar nan, wato ana cike gibi da wadannan kudade da aka kwato.  Muna fatar Allah ya wayar da kan gwamnatin Nijeriya ta yi amfani da kudade da ta kwato wajen yi wa al’ummar kasar nan ayyuka. Domin a kullum talakawa suna kukan cewa ba su gani a kasa ba.

  Abin da muke so shi ne gwamnatoci  su yi wa jama’a aiki. Yanzu hanyoyin Nijeriya a lalace suke. Makarantunmu da asibitocinmu a lalace suke, kamfanoninmu a durkushe suke. Miliyoyin daliban Nijeriya  sun gama makaranta babu aikin yi. Babu yadda za a yi a ci gaba a Nijeriya a irin wannan hali.

  GTK; A kwanakin baya shugaban kasa ya gabatar wa da ‘yan majalisun tarayya kasafin kudi na sabuwar shekara mai kamawa, a matsayinka na masani kan harkokin noma ya ya kake ganin kason da aka ware wa harkokin noma a wannan kasafin kudi?

  Farfesa Dadari; A gaskiya a wannan kasafin kudi ba a dauki noma da muhimmanci ba, kamar yadda aka yi a sauran kasafin kudin Nijeriya na shekarun da suka gabata. A tsarin majalisar dinkin duniya duk kasar da take son ta ci gaba, dole ne ta bai wa harkokin noma mahimmanci a kasafin kudinta, akalla ana son kowace kasa ta bai wa harkokin noma kashi 15 zuwa 25. Saboda an dauki noma kamar wata shinfada ce ta ci gaba da yalwata da tasiri.

  Don haka ko kasashen da suka ci gaba kamar Amerika da Burtaniya ba su ci gaba ba sai da suka bunkasa harkokin noma. Abin da ya sa noma ya sami matsala a Nijeriya shi ne sanya kabilanci a cikin kasafin kudinmu. Wato kabilancin da muke sanyawa a cikin kasafin kudi shi ne ni idan ba za a yi abu a wajenmu ba, ba zan goyi baya ba.

  Yanzu a jihohin arewa muna da yanayi da kasar noma mai kyau. Abin da yake faruwa idan aka gabatar da kasafin kudi dan kudu baya goyan bayan a baiwa harkokin noma karfi a kasafin kudin Nijeriya, saboda ba a noma a yankinsa.

  Don haka ‘yan majalisun arewa ne ya kamata su tsaya su kare harkokin noma a majalisa, domin a bai wa harkokin noma kaso mai tsoka a kasafin kudin kasar nan. Domin suna wakiltar mutanen arewa ne, wadanda noma da kiwo ne karfinsu. Don haka duk abin da ya shafi noma da kiwo ya kamata ‘yan majalisun arewa su ba shi muhimmanci.

  Kuma ko wane ne yake mulki a kasar nan, idan ya ga Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya na arewa sun tsaya kan a ware wa harkokin noma kaso mai yawa dole ne zai yi.

  Don haka ‘yan majalisar arewa suna sane cewa an saukar da harkokin noma kasa a kasafin kudin shekara ta 2018, don haka ya kamata su tashi su yi magana domin a halin yanzu wannan kasafin kudi yana nan a gabansu.

  Kuma ya kamata ‘yan Nijeiya baki daya wato ‘yan majalisun na arewa da kudu su sani cewa yanzu ana bai wa noma muhimmanci a duniya. Domin suna zuwa kasashen waje suna ganin yadda ake bai wa harkokin noma muhimmanci. Don meye ba za su hada kai a bai wa harkokin noma muhimmanci don arzikin Nijeriya ya rayu ba?. Domin idan ba an inganta noma ba, tattalin arzikin Nijeriya ba zai taba rayuwa ba.

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here