SARAKUNA NA HADA KAWUNAN JAMA\’A –ETSU NUPE

0
901
MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
MAI martaba Etsu Nupe Dokta Alhaji Yahaya Abubakar ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na arewacin kasar nan tare da takwarorinsu na kudanci nayin iyakacin bakin kokarin sun a hada kan al’umma domin a zauna lafiya da ci gaban kasa.
Etsu Nupe ya bayyana haka zantawarsu da wakilinmu na kudanci  a kalaba ranar Asabar makon day a gabata lokacin da ya halarci bikin kaddamar da littafin tarihin wani babban dan siyasa mai suna Godwin Jeddy Agba, da aka yi wanda mai martabar ya kasance shi ne babban bako mai jawabi a bukin.
Etsu Nupe yaci gaba da cewa “mu sarakunan gargajiya muna taka mahimmiyar rawa tsakaninmu da takwarorinmu na kudanci wajen kwantar da hankali al’ummarmu da kuma al’ummar kudancin kasar nan mazauna arewa domin a samu hadin kan kasa da kuma zama lafiya mu a arewa muna bakin kokari wajen kare musu martabar su da kuma ba su isasshiyar damar su yi walwala su sake musamman masu gudanar da harkokina kasuwa ko kuma wadanda aikin ya kai arewa don haka muna tattaunawa a tsakaninmu da takwarorin mu na kudanci. inji shi
Dokta Alhaji Abubakar yaci gaba da cewa “baya da samar  zaman lafiya muna kuma kara tabbatar da kasancewarmu kasa daya kuma matsayinmu bayan kare martabar kowane dan Nijeriya ba za mu taba bari kasar nan ta wargaje ko kuma rabu ba duk wani abu da zai kawo wargajewar zamantakewarmu matsayinmu na sarakuna iyayen  al’umma ba za mu yarda da shi ba”.
Karshe ya bukaci a mutunta zamantakewa tare da ba kowa ne dan kasa ‘yancin zama a duk inda yake so ya yi walwala ko sana’a ba tare da an kuntata masa ba domin “Allah ya riga ya hada zamanmu wuri guda kuma tsarin mulkin kasar nan ya ba kowane dan Nijeriya damar ya zauna Inda yake so ya yi kasuwancinsa ko aiki tare da gudanar da addininsa da duk yake bi ba tare da wata tsangwama ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar masa”.inji Etsu Nupe.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here