\’YAN SANDA NA TSARE DA MATAR DA TA KASHE DANTA

0
837

 

 

 RUNDUNAR ‘yan sandan jihar Ebonyi tana tsare da Ahmed Ajibore da matarsa mai suna Chidimma da ke layin Obubra ,Abakalike tana musu bincike sakamakon zarginsu da ake yi mijin ya umarci matarsa ta makure dan su dan wata takwas da haihuwa mai suna Emmanuel har ya mutu.
Wannan lamari ya faru a garin Abakalike hedkwatar jihar.
Wata majiya da ke unguwar take makwabtaka da magidantan da ta  nemi a sakaya sunanta ta ce  “shi Ajibore , ne da kansa ya umarci matar tasa Chdimma ranar Talata da ta makure yaron har sai ya mutu hakan kuwa aka yi”.Da take yi wa manema labarai karin bayani Chidimma uwar yaro Emmauel ta ce Ahmed mijinta a dare ya ba ta kudi Naira Dubu 3 da wata guntuwar igiya ya ce ta yi amfani da ita ta makure wuyan yaron har sai ya mutu.
Itama Lovely Nwode ‘yar uwar Chidinma da take bayar da shaida wurin ‘yan sandan ta ce “sabani suka samu tsakanin Ahmed Ajobore wanda shi makanike ne da ‘yar uwar tata shi ya sa ya bayar da umarnin ta kashe yaron.inji ta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi  ASP Loveth Odah, ta tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna hannu ana binciken su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here