GOBARA TA LASHE MOTOCI 49 A MASANA\’ANTAR  GYARAN MOTOCI TA  KWAKWACIN DAWANAU.

0
763
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
GOBARA ta cinye kawunan manyan motoci har 49 a masana\’antar gyaran motoci ta kwakwacin Dawanau tare da lalata wasu kayayyaki da ke kusa da gurin da aka ajjiye kawunan motocin.
Wakilinmu wanda ya ziyarci wannan masana\’anta ta kwakwacin Dawanau  ya ruwaito cewa gobarar ta yi barna mai yawa inda  kawunnan manyyyan motoci na miliyoyin nairori suka kone tun kafin a sami damar kashe wannan gobara wadda ta tashi cikin daren Talatar data gabata.
Daya daga cikin shugabannin gurin Alhaji  Zahiru Umar ya shaida wa GTK cewa cikin dare gobarar ta tashi lokacin da babu kowa sai \’yan bangar da suke kula da masana\’antar, inda ya ce al\’uma sun yi matukar kokari wajen ganin an kashe wannan wuta bisa taimakawar jami\’an kashe gobara wadda ta yi barna mai tarin yawa.
Sannan ya sanar da cewa  dumbin mutane da ke gudanar da harkokinsu na neman abinci a wannan masana\’anta ta  kwakwaci wanda a cewarsa akwai mutane fiye da dubu biyar da a kullum suke harkokin su na dogaro da kai a gurin kuma kowa yana aikin sa bisa gaskiya da rikon amana.
Haka kuma Alhaji Zahiru ya yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ga baturen yan sanda na yankin karamar hukumar Dawakin Tofa da jami\’in shiyya na rundunar yansan da  sakatare na kungiyar  kanikawa wato NATA da shugaban kungiyar na jiharr kano da kuma shugaban kungiyar na ahiyyar arewa maso yamma da dukkanin mutanen da suka ziyarce su domin yyi masu jajen wannan gobara da suka yi.
Da yake karin bayani kan wannan guri, jami\’in hulda da jama\’a na kungiyar kanikawa ta kwakwacin Dawanau Alhaji Bala Dahiru ya bukaci gwamnatin jihar Kano da majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa da su hada hannu wajen kara bunkasa wannan masana\’anta wadda ake matukar alfahari da ita a fadin nahiyar Afirka,  inda ya nunar da cewa akwai bukatar a samar da wutar lantarki a gurin da kewaye wajen domin inganta tsaro domin inganta shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here