PDP Ta Zabi Uche Secondus Sabon Shugabanta

0
831

Rabo Haladu Daga  Kaduna

AN bayyana Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam\’iyyar adawa ta PDP, a babban taron da aka yi tsawon daren Asabar ana kidaya kuri\’u.
Da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban kwamitin zabe, Mista Gabriel Suswam, ya ce Uche Secondus ya kayar da abokan takararsa uku bayan ya samu kuri\’a 2000 cikin kuri\’a 2,296 da aka kada.
Hakazalika, an zabi Sanata Umar Ibrahim a matsayin sabon Sakataren jam\’iyyar na kasa yayin babban taron na Abuja, kuma tuni aka rantsar da sabbin shugabannin don kama aiki.
Mahalarta babban taron dai sun zabi sabbin jami\’an da za su ja ragamar jam\’iyyar kan mukamai guda 21 ne.
Tun da farko dambarwa ta kunno kai bayan wasu sun yi zargin shirya magudi, lokacin da wata takarda ta rika zagaya hannun mahalarta taron dauke da jerin sunayen wasu \’yan takara.
Prince Secondus ya taba rike jam\’iyyar PDP a matsayin shugabanta na riko, bayan Alhaji Adamu Mu\’azu ya yi murabus lokacin da aka kayar da ita a babban zaben 2015.
Wani tsohon ministan ilmi, Tunde Adeniran ne ya zo na biyu da adadin kuri\’a 231, a lokaci guda kuma hamshakin mai harkar kafofin yada labarai, Raymond Dokpesi ya samu kuri\’a 66.
Tun da farko, Mista Dokpesi ya bayyana adawa da take-taken da ya kira na tafka magudi, bayan bayyanar takarda mai dauke da sunayen wasu \’yan takara da aka kira \”sunayen \’yan takarar hadin kai\”.
Ya ce wani dan takara ya zo gare shi yana kuka, inda yake ce masa tsarin zaben ba zai tabbatar da ganin an yi gaskiya da adalci ba. Dokpesi ya bayyana zaben da cewa baba-rodo ne kawai.
Baya ga Raymond Dokpesi akwai karin wasu \’yan takara da suka bukaci a soke zaben, saboda magudin da suka ce sun lura da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here