GODIYA GA GWAMNAN JIHAR KANO

0
989
Gwamna Ganduje Na Jihar Kano
INA mai farin cikin yin amfani da wannan kafar yada labarai domin in mika godiya ta musamman ga mai girma gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda aikin hanyar da ta tashi daga Yar Gwanda zuwa Kafayau zuwa Rage ta wuce zuwa Tatsan  zuwa Rinji da Unguwar Bakke har Daddarawa.
Wannan hanya an dade ana neman a yi ta amma sai a wannan lokaci na gwamnatin Gwamna Ganduje muka sami nasarar aiwatar da ita domin hanyar tana da matukar muhimmancin gaske ga al\’umomin da ke wannan bangare mai albarka, sannan dukkanin mutanen da ke garuruwan da hanyar ta ratsa suna masu alfahari da wannan gwamnati  wadda take aiki bisa yin la\’akari da bukatun jama\’ar kowane yanki.
Babu shakka idan har Allah ya sa aka kammala wannan hanya za mu sami saukin zirga-zirga da fitar da kayan amfanin gona daga yankunan namu zuwa sauran gurare kamar yadda muke gani a sauran gurare,  sannan ina kara godiya ga dukkanin wadanda suke da hannu wajen tabbatar da ganin an sanya hanyar tamu cikin jerin hanyoyin da ake yi a fadin jihar Kano a wannan gwamnati mai albarka.
Daga Bala Dahiru Tatsan, PRO na  masana\’antar gyaran motoci ta Kwakwacin Dawanau karamar hukumar Dawakin Tofa Kano.
08036828169,07046406277

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here