A wannan hoto za a iya ganin diyar iyalan Alhaji Adamu Yusuf wadda ta rage a raye, wato Amina Adamu Yusuf. Ita ba ta kwana a dakin nasu ba ta kwana ne a wajen kakanninta, Allah Ya kaddara babu ita a cikin hadarin gobarar. Allah Ya raya mana ita cikin addininSa, ya ba ta da sauran dangi hakurin wannan rashi, amin.
Isa Ahmed ne ya aiko mana da hotunan.