Daga 2008 Zuwa 2016 An Kama Jiragen Ruwa 200 A Tekun Najeriya

    0
    1352

    Rabo Haladu Daga Kaduna

    AN kammala taron kungiyar G7 na wasu kasashen yammacin Afrika da Turai da ke gabar tekun Guinea, wanda aka kafa domin samar da tsaro a yankin tekun na tsakanin kasashen.
    An gudanar da wannan taron ne a jihar Legas  wacce take daya daga cikin mambobin kungiyar. Mahalarta taron
    sun yanke shawarar daidaita dokokin kasashen da ke cikin hadakar da nufin gaggauta hukunci da kuma kawo karshen ayyukan fasa-kwauri da fashin cikin teku a yankin ruwan na Guinea, kamar yadda Mista Alan Charles na
    Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.
    Ya kuma bayyana cewa akwai ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniyan da suka kai akalla guda hamsin da ke wannan yankin tekun. Wata ma’aikaciyar shari’a  Hajiya Hajara Yusuf na cikin masu jawabi a wajen taron, don bayyana matsayin da kasarta ke ciki na daukar matakan shari’a a kan wadanda ake damkewa da laifi.
    Shi ma wani jami’in sojan ruwa Adimiral Ferguson, kwamandan horarwa a rundunar sojan ruwan ta ta kasa ya bayyana cewa sun zage damtse don magance fashin teku. Inda ya bayyana cewa daga shekarar 2008 zuwa ta 2016 an kama jiragen da ke da laifi akalla guda dari biyu, amma wadanda aka hukunta ba su wuce guda goma sha biyar ba.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here