Yan Shi\’a Suna Zanga- Zangar Kwanaki Uku A Abuja

0
973

Rabo Haladu Daga Kaduna

MABIYA tafarkin shi\’a daga sassa daban-daban na kasar nan suka fara wani gangami na kwanaki uku a birnin Abuja
don nuna juyayin rikicinsu da sojoji a Zariya.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan rikicin ‘yan shi’ar ne da sojojin a Zariya aka cafke shugaban nasu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky bayan rasa rayukan mabiyan malamin da dama ciki har da ‘ya’yansa da aka zargi sojojin da kashe su.
A watannin baya wata kotu ta ba da umarnin sakin Shehin malamin tare da gina masa sabon gida a inda yake so sakamakon rushe masa muhallin da aka yi.
Bugu da kari kuma a bashi diyyar miliyoyin nairori sakamakon cin zarafin da aka yi masa. To amma duk da wannan hukuncin na kotun, sakin El- Zakzaky ya ci tura. Wanda hakan ce ta sa mabiyan nasa ke ta zanga-zangar lumana don ganin an sake shi.
Ko a wannan ranar ma, mabiyan na El-Zakzaky sun bayyana cewa za su ci gaba da zanga-zangar lumana har sai
an ji kukansu bisa dokar sakin malamin nasu da aka zartar amma jami’an gwamnati da alhakin sakin nasa ya rataya a kansu suka yi burus da lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here