Rabo Haladu Daga Kaduna
KOTUN daukaka kara ta yankin Abuja ta tasa keyar shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki, zuwa kotun da\’ar ma\’aikata domin a sake masa sharia kan zargin rashin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa.
Gwamnatin tarayya dai ta daukaka kara ne bayan kotun da\’ar ma\’aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan farkon wannan shekarar.
Kotun da\’ar ma\’aikatar ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume 18 na rashin fadin gaskiya wajen bayyana kadarori da aka yi wa Saraki
A zamanta a yau, kotun ta yanke hukuncin cewa Mista Saraki bai bayar da gamsasshiyar amsa kan uku daga cikin tuhume-tuhume 18 da ake yi masa ba.
Masu shari\’ar uku da suka jagorancin zaman kotun karkashin alkali Tinuade Akomolafe-Wilson, sun yi watsi da sauran tuhume-tuhume 15 din da gwamantin ta yi wa Saraki.
Sai dai kuma a wata sanarwa daga ofishin watsa labaran Bukola Saraki ta ce shugaban majalisar dattawan ya ce zai daukaka kara kan hukuncin.
Shi kuwa lauyan gwamnati kan shari\’ar, Rotimi Jacobs, ya ce zai yi nazari kan hukuncin kotun kafin ya yanke shawara kan matakin da zai dauka.