KUNGIYAR NCWS ZA TA CI GABA DA KYAUTATA RAYUWAR MATAN NIJERIYA- INJI HAJIYA ZAINAB ALI MUSA

0
917
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SHUGABAR kungiyar matan Nijeriya ta kasa  wato (NCWS) reshen Jihar Kano Hajiya Zanab Ali Musa ta ce kungiyar tasu za ta ci gaba da bullo da kyawawan shirye-shirye  domin ganin mata da yara kanana suna cikin yanayi mai kyau walau a yankunan karkara ko a birane.
Ta yi wannan tsokaci ne a zantawarsu da wakilinmu, inda ta sanar da cewa mata su ne iyayen al\’umma kuma suna bukatar kulawa ta musamman ta yadda za su ci gaba da ba da tasu gudummawar wajen ci gaban kasa da wanzar da zaman lafiya kamar yadda suke yi a halin yanzu.
Sannan ta nunar da cewa yanzu lokaci ya yi na a kara bai wa matan kasar nan damar taimaka wa gwamnatoci wajen aiwatar da wasu shirye-shirye wadanda aka fito da su domin tabbatar da ganin an sami nasarar gudanar da su kamar yadda ake bukata, tare da fatan cewa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi har ma da na kananan hukumomi za su kara shigar da mata cikin shirye-shiryensu bisa la\’akari da rikon amanarsu.
Hajiya Zainab Ali Musa ta kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba wa uwargidan shugaban kasa Hajiya A\’isha Muhammadu Buhari saboda kokarin da take yi wajen samar da yanayi mai kyau ga matan kasar nan da kuma yara kanana ta cikin shirinta na \”future assured\” wanda a cewar ta wannan shiri ya bude hanyoyin dogaro da kai ga mata a kowane lungu da sako na wannan kasa tamu.
A karshe, Hajiya Zainab ta isar da sakon kungiyar NCWS reshen Jihar ta Kano ga gwamnatin Jihar Kano da masarautar Kano da daukacin al\’ummar jihar bisa ziyarar aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi cikin nasara, tare da jaddada cewa kungiyar tasu za ta ci gaba da taimaka wa mata ta hanyoyi daban-daban domin  ganin suna cikin farin ciki a kodayaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here