Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
KWAMISHINAN ma\’aikatar lafiya a Jihar Yobe Alh Bello Kawuwa ya
tabbatar da cewar an samu mutane 10 da ke dauke da cutar nan ta
sankarau a cikin jihar kuma, 3 daga cikinsu tunin sun riga mu gidan
gaskiya.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar gangamin
allurar riga-kafin cututtukan nan na kyanda da sankarau da ke yaduwa a
cikin al\’umma musamman a lokacin zafi da aka gudanar a garin Damaturu.
Ya kara da cewar, gwamnatin Jihar da hadin gwiwar hukumar samr da
harkokin kiwon lafiya a matakin farko ta kasa
(PHC).
Kwamishinan ya ci gaba da cewar, wannan riga-kafin da ake kokarin a kai za
a gudanar da shi ne a cibiyoyin kiwon lafiyar da aka tanada, ana kuma
kyautata zaton za a yi wa yara kimanin 771,778 riga-kafin.
Ya kara da cewar wannan aiki na riga-kafin za a gudanar da shi ne
bangare biyu na farko tunin aka fara gudanar da shi daga ranar 7 ga
watan nan na Fabrairu 2018 aka kare shi a ranar Lahdi 11 ga wata a
kananan hukumomi 8 sai kashi na biyu a gudanar da shi daga ranar 14 ga
watan na Fabrairu zuwa 18 ga watan.
Don haka ne kwamishinan ya nemi iyaye da su bada \’ya\’yansu don yi musu
wannan riga-kafi don hakkinmu ne mu iyaye da mu ga mun samarwa da
yaranmu yanayin lafiya mai nagarta.