KWASHE \’YAN MATAN SAKANDAREN DAPCHI YA JAWO CECE KUCE TSAKANIN GWAMNAN YOBE DA BANGAREN TSARO

0
652
Gwamna Gaidam: Sha yabo katafila sarkin aiki

Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu

HARIN  da wasu \’yan bindigar da ake kyautata zaton \’yan kungiyar Boko

Haram ne su ka kai a makarantar sakandaren \’yan mata ta kimiyya da

fasaha da ke garin Dapchi cikin karamar hukumar Bursari a Jihar Yobe

da ya yi sanadiyyar yin awon gaba da dalibai mata akalla 110 ya jawo

cece-ku-ce a tsakanin Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam da kuma

bangaren tsaron kasa.

A rahoton da wakilinmu ya ruwaito na nuna cewar, wannan takaddama

tsakanin Gwamna Gaidam da kuma bangaron dakarun kasa ya taso ne

sakamakon bayanin da Gwamnan ya yi lokacin da shugaban kungiyar

Gwamnonin arewa Alhaji Kashim Shettima na Jihar Borno ya kai masa

ziyarar jaje a madadin kungiyarsu cewar, ko daya biyu babu wannan hari

da aka kai a makarantar \’yan mata ya faru ne sakamakon janye jami\’an

tsaron sojan da ke garuruwan Dapchi da Baimari kasa da sati biyu.

Gwamna Ibrahim ya ci gaba da cewar, in da har sojoji na garin na

Dapchi ba a janye su ba tabbatacce ne wadannan maharan da ba za su

gwada kawo wannan hari ba tare kuma da samun nasarar tserewa da

dalibai mata akalla 110 kamar yadda sahihan alkaluma suka nuna.

Ya kara da cewar, ire-iren hakan ya sha faruwa a Jihar ta Yobe, a

cewar gwamnan a shekarar 2014 hakan ya faru a garin Buni Yadi yadda

kasa da kwanaki 2 da janye sojoji a gab da makarantar sakandare

gwamnatin tarayya (FGC) sai ga \’yan Bokn sun kai harin da ya yi

sanadiyar kashe dalibai sama da 20. Haka aka yi a makarantar koyon

aikin gona dake Gujba wadda aka yanka tare da kona dalibai masu yawan

gaske.

Don haka gwamnan ya kirayi bangaren na tsaro da su gaggauta dawo da

jami\’an tsaro a wuraren da aka janyesu musamman agaruruwan da ake

zaton suna fuskantar barazanar tabarbarewar harkokin tsaro da kuma

garuruwan dake da makarantun sakandare na mata ko na maza.

Idan ba a manta ba a ranar litinin ta mako jiya ne dai \’yan bindigar da

ake kyautata zaton \’yan kungiyar Boko Haram ne suka yi awon gaba da

daliban makarantar sakandaren \’yan mata na garin Dapchi wadda hakan ya

jefa al\’umma cikin dimuwa da tunanin lamarin ya zama tamfar wata

boyayyar manufa kasancewar wadannan \’yan kungiya babu abin da suka

dauka in banda wadannan \’yan mata kamar yadda mafi yawa-yawan

al\’ummomi ke cewa.

Malam Bashir Dapchi wadda na daga cikin iyayen da lamarin ya shafa

kuma shugaban kungiyar wadanda aka dauke \’ya\’yansu shi ma ya yi irin

wannan korafi da gwamna Gaidam ya yi. A cikin jawabinsa ga wakilinmu

ya ce lalle dauke yaransu ba komai bane illa sakacin harkokin tsaro,

don da akwai sojoji a lokacin lalle da wadannan mahara ba su samu

nasarar dumfarar makarantar ba ma ballantana su dauke yaran.

Don haka ya yi roko ga gwamnatin tarayya da ta yi hobbasan kwato musu

yaransu a cikin lokaci tun kafin lamarin ya yi zurfi irin na \’yan matan Chibok.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here