Daga JABIRU A HASSAN, Kano.
BABU shakka, kowa yasan cewa fannin kula da lafiya yana da matukar muhimmancin gaske musamman ganin yadda al\’uma take kara yawaita a kowace rana.
Sannan kowa yasan gwamnatocin kasarnan suna kokari kwarai wajen tabbatar da cewa gannin kula da lafiyar jama:a yana samun kulawa ta musamman duk kuwa da irin kalubalen dake tattare da wannan fanni.
Haka kuma a kowane fanni akwai wasu mutane da Allah ya zaba kuma ya basu wata basira ta aiwatar da aiki wanda suka kware akai musamman kan kiwon lafiya da aiwatar da wasu manufofi ko tsare-tsare wadanda gwamnatoci suke fito wa dasu cikin nasara.
A fannin kula da lafiya ma akwai kwararrun likitoci wadanda Allah ya baiwa kaifin basirar aiki ko tafiyar da aikin kula da lafiya ko kuma jan ragamar wani bangare na fannin kula da lafiya batare da an sami wata miskila ba irin su Dokta Nafi\’u Yakubu Muhammad Tofa, wanda ya yi fice wajen aiwatar da aiki a matsayin sa na likita kwararre.
Sannan yana da wata gogewa wadda take bashi damar gudanar da aikin likitanci da shugabancin cibiyoyin kula da lafiya ko aiwatar da wasu manufofi na gwamnati kan sha\’anin kiwon lafiya kamar yadda ake bukata, wanda hakan ce ma tasa Dokta Nafi\’u Yakubu Tofa ya kasance likita wanda Allah madaukakin sarki ya yi wa baiwa kan aikin kula da lafiya tun lokaci mai tsawo.
Bisa haka ne ake yi wa Dokta Nafi\’u kallon kwarewa kan aikin likita, wanda kuma ya cancanci rike kowane irin matsayi walau a matakin jiha ko kasa a fannin kula da lafiya bisa la\’akari da baiwar da ubangiji yayi masa kan aiki.
Sannan yana da kyau gwamnati ta kara duba irin kokari da kwazon aiki da kuma rikon amanar da likita Dokta Nafi\’u Tofa ke yi kuma a fannin kula da lafiya a Jihar Kano, wanda yanzu haka shine babban likita a babban asibiti na Imamu Wali dake Kabuga ta Jihar Kano, sannan kwararre a fannin aiwatar da manufofi wadanda suka shafi kiwon lafiya.
Daga karshe, al\’uma suna fatan cewa gwamnatin jihar kano zata duba gudummawar da mutane irin su Dokta Nafi\’u Tofa suke bayar wa kan fannin kula da lafiya domin a ba su amanar wasu gurare don aiwatar da manufofin gwamnati kan kiwon lafiya.
Jabiru A Hassan, shi ne wakilin jaridun New Nigerian a Kano, kuma za a iya samun sa a wadannan layuka: 08039640882, ko 08083381966, ko adireshin sa na e-mail: jabiru.hassan@yahoo.com