Daga Usman Nasidi
TSOHON shugaban kasar Najeriya a mulkin soji da farar hula, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewar har yanzu akwai wani abu dake matukar damun sa duk lokacin da ya tuna da shi.
Obasanjo, mai shekaru 81 a duniya, ya ce babban abinda yake nadama da takaici shine rashin dogon kwanan iyayen sa.
Obasanjo na wadannan kalamai ne a yau, Litinin, yayin da ya cika shekaru 81 da haihuwa.
Tsohon shugaban kasar ya ce, ya so a ce iyayen sa sun yi nisan kwana domin ganin irin nasarorin da ya samu a rayuwa.
\” Wani abu daya da nake matukar nadama da takaicinsa shi ne yadda iyayena suka mutu da wuri. Basu tsaya sun ci moriyar wahalar da su ka sha a kaina ba. Na so a ce sun yi nisan kwana, sun ci moriyar wahalar su ,\” inji Obasanjo.
Obasanjo ya ce ya yarda da karin maganar nan Yoruba da su ke cewa \”wadanda su ka mutu na yin waiwaye domin ganin abinda su ka bari a duniya\”.
Obasanjo ya kara da cewar, riko da wannan karin magana ne kawai ke kwantar ma sa da hankali, domin a cewar sa, ya san iyayen sa na cikin farinciki a kabarinsu, yayin da suke kallon irin nasarorin da ya samu a rayuwa.
Obasanjo ya ce zai ci gaba da bauta wa Allah da yin addu\’o\’i ga iyayensa. Kazalika ya yi godiya ga hadimansa da kuma mataimakansa