MUN  YI GODIYA GA AL\’UMAR KARAMAR HUKUMAR DAMBATTA- Musa Sani

    0
    707
    JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
    MATAIMAKIN shugaban karamar hukumar Dambatta Alhaji Musa Sani Dambatta ya nuna godiyar sa ga al\’umar karamar hukumar ta Dambatta saboda kaunar da suke nuna masu a zaben kananan hukumomin da ya gabata.
    Ya yi wannan tsokaci ne cikin sakon fatan alheri da ya gabatar wa al\’ummar yankin bisa goyon bayan da suke basu tun daga yakin neman zabe har zuwa lokacin da aka rantsar da su domin fara aiki a matsayin zababbun shugabannin  wannan yanki.
    Alhaji Musa Sani ya kuma nunar da cewa za su yi bakin kokarin su wajen ciyar da karamar hukumar Dambatta gaba tareda samar da rayuwa mai inganci ga  al\’umar yankin bisa la\’akari da bukatun su batare da nuna bambancin siyasa ko na ra\’ayi ba, musamman ganin cewa shugaban karamar hukumar  watau Alhaji Idris Haruna Zago mutum ne mai kishin al\’umar sa ta kowane fanni.
    Haka kuma ya yi bayanin cewa za su hada hannu da dukkanin shugabannin yankin da jagororin siyasar yankin da kuma sarakunan gargajiya kama daga kan hakimi zuwa dagatai da masu unguwanni da kuma malaman yankin ta yadda kwalliya za ta ci gaba da biyan  kudin sabulu, inda kuma mataimakin shugaban karamar hukumar ta Dambatta Alhaji Musa Sani yayi fatan alheri ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa daurin auren \’yarsa Hajiya Fatima da aka gudanar tareda fatan Allah ya sanya albarka cikin lamarin.
    A karshe, Alhaji Musa Sani Dambatta ya godewa daukacin ma\’aikatan karamar hukumar ta Dambatta saboda kokarin da suke yi da kuma irin gudummawar da suke bayarwa wajen ganin yankin yana samun ci gaba mai amfani batare da nuna gajiyawa ba.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here