Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
A kokarin Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i, na ganin an magance rikice rikicen kabilanci da samun yamutsi an gabatar da mutane 65 gaban kotun majistare da ke Titin Daura.
Ita dai Gwamnatin Kaduna ta bakin mai magana da yawun Gwamnan Mista Samuel Aruwan cewa ya yi game da batun rikicin kasuwar Magani a satin da ya gabata, yasa a ranar Juma ar da ta gabata aka gurfanar da mutane Sittin da biyar gaban kotun majistare da ke Titin Daura a cikin garin Kaduna.
An Kuma saka ranar sha biyar ga wannan watan domin ci gaba da shari\’a.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa ana kokarin ganin an magance matsalar samun shafaffu da mai idan an samu matsalar rikici a ko Ina a Jihar .
Samuel Aruwan ya aike da sakon cewa duk Wanda ya tayar da fitina sai an hukunta shi kamar yadda Doka ta tanadar.