WASU \’YAN MAJALISA ZA SU KALUBALANCI SHUGABA BUHARI A KAN PEACE CORP

0
862
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki
Daga Usman Nasidi
WASU \’yan majalissar wakillai sun shirya kalubalanatar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin wannan makon akan kin rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’
Wasu ‘yan majalissar kasar Najeriya sun fadawa manema labaru cewa za su dauki mataki akan kin amincewa da rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’ da Buhari yayi, saboda irin kokarin da suke yi wajen tatance hukumar a shekarar da ta gabata.
\’Yan majalisar Najeriya sun shriya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa hukumar Peace Corps.
‘Yan majalissa dattijai da dama sun bayyana takaicin su a kan wannan al’amari, inda mafi akasarin su suka ce, kafa hukumar zai gyara siyasar su kafin zabe mai zuwa.
Mai magana da yawun bakin majalissar dattijai, Sanata Sabi Abdullahi, ya ce majalissar dattijai za ta yi amfani da karfin da dokar kasa ta bata wajen kafa hukumar Peace Corps idan shugaban kasa ya kara kin rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here