AN KADDAMAR DA KUNGIYAR TAKARAR BUHARI DA EL’RUFA’I TA 4+4 RESHEN KARAMAR HUKUMAR LERE

    0
    820

    Isah Ahmed  Daga Jos

    A yayin da zabubbukan shekara ta 2019 da za a gudanar a Nijeriya,  suke kara gabatowa. An gudanar da taron kaddamar da kungiyar magoya bayan sake tsayawa takara, ta shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasiru El’Rufa’i  a zabubbukan na shekara ta 2019, mai suna 4+4 reshen karamar hukumar Lere  da ke jihar Kaduna.

    Shi dai wannan taro wanda aka  gudanar da shi ne a garin Saminaka, ya sami halartar shugabannin wannan kungiya daga  sassa daban daban na jihar Kaduna.

    A nasa jawabin a wajen wannan taro, shugaban matasan wannan kungiya na jihar Kaduna, Alhaji Mas’udu Yusuf Ahmed Saminaka ya bayyana cewa ganin irin ayyukan  da shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i suka faro, ya sanya suke son su sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019.

    Ya yi kira ga al’ummar jihar Kaduna da  Nijeriya baki daya, su dubi irin ayyukan ci gaba, da wadannan shugabanni suka kawo a cikin shekaru uku da suka yi suna kan mulki.

     Shi ma a nasa jawabin, wani jigo a jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Lere, Kwamared Sunusi Sufwan ya yi bayanin cewa ganin  yadda al’ummar qaramar hukumar Lere suka fito suka rungumi wannan qungiya, ya nuna cewa sun gamsu da irin ayyukan da gwamnan  jihar  Kaduna yake yi a  qaramar hukumar.

    Kwamared Sunusi Sufwan ya yi bayanin cewa ya zuwa yanzu a nan ana aikin hanyoyi a cikin garin Saminaka da aikin hanyar da ta hada jihar Bauci da garin Saminaka. Kuma  an kashe miliyoyin naira wajen gyara kwalegin gwamnati da ke Saminaka, baya ga aikin   gyaran makarantun firamare da asibitoci da ake yi  a qaramar hukumar.

    Don haka ya ce ya zama wajibi ga al’ummar karamar hukumar  su zabi Gwamna Nasiru El-Rufa’i  da shugaban kasa Muhammad Buhari domin su kaxai ne masu akidar son gyara Nijeriya.

    A nasa jawabin mataimakin shugaban dattawan jam’iyyar APC a karamar hukumar Lere Alhaji Tanimu Ahmed Kunkuru  ya yaba wa shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i-

    Ya ce gaskiya tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a jihar Kaduna, ba a tava samun gwamnan da yake son ya taimakawa talakawa a jihar  kamar gwamna  Nasiru El-Rufa’i ba. Ya ce zuwan Gwamna Nasiru El-Rufa’i  ya buxewa talakawa ido a jihar ta Kaduna, ta hanyar gudanar da ayyukan raya qasa kamar gina makarantu da  hanyoyin mota da gadoji da asibitoci.

    Alhaji Tanimu Kunkuru ya yi bayanin cewa badan zuwan shugaban qasa Muhammad Buhari ba, da yanzu al’ummar Nijeriya ba su san halin da muke ciki ba, saboda matsalar tsaro. Ya ce  amma da zuwansa tsaro da noma da  tattalin arziqi suka inganta a Nijeriya.

     

     

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here