JUYIN-JUYA-HALI A BANGAREN ILMIN JIHAR SAKKWATO

  0
  3116
  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

  TSARARREN tsari mai kyau a bangaren ilmi ko shakka babu yana daya daga cikin muhimman al’amuran da suka shafi ci gaban walwala da na tattalin arzikin kowace kasa.

  Ilmi shi ne tamkar a fagen yaki, garkuwar kariyar talauci. Yana bai wa mutum sanin da ya dace da wasu hazakoki daga gare shi wadanda yana amfani da su, kuma yana samun saukin gudanar da rayuwarsa. To, dalilin hakan ne gwamnatoci na Duniyar nan suke mayar da hankulansu kacokan ga wani kaso mai tsoka na kudadensu domin ganin ci gaban wannan bangaren na ilmi.

  Sashe mai kula da ilmi na majalisar dinkin duniya, wato UNESCO ya bayar da wani rahoto da ke cewa, ‘’kasar Nijeriya ce ta dara kowace kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Rahoton ya nuna yara kimanin Miliyan goma da rabi (10.5 ) a Nijeriya ne ba su zuwa makaranta. Haka kuma shirin nan na ba da ilmi ga kowa ( EFA ) su ma rahotonsu haka ya nuna cewa, ‘’akwai rashin daidaito na jinsi a wadansu bangare na kasar ta Najeriya’’.

  Kafin zaben shekarar 2015 da ya kawo shugabancin Gwamna mai ci yanzu, Rt. Honorabul Aminu Waziri Tambuwal a matsayin zababben Gwamna, kididdiga a sashen ilmin Jihar Sakkwato babu wani abin-a-zo-a-gani ko burgewa cikinsa, akwai karancin karbabbiyar hanyar koyarwa ta duniya wanda ya yi hannun riga da irin bukatar da ake nema a wajen yawancin Masanan ilmi, sannan ga balbalcewar tsarin koyarwar a ciki da wajen jihar nan.

  Shigarsa ofis ke da wuya, Gwamnan ya fara tunanin tsare-tsarensa da hanyoyin da zai bi domin sauya akalar tsarin bangaren na ilmi, inda ya zuwa yau din nan Allah Ya taimake shi ya farfado da sashen na ilmin, kuma ya zama kyakkyawan abin koyi ga sauran jihohi.

  Takun sakar da ya biyo bayan juyin-juya-halin da shugabancin Tambuwal ya samu a bangaren nan na ilmi ba abin da za a fede biri har wutsiyarsa ba ne, sai dai kawai dalilin al’ummar Sakkwato wadanda tuni suke cike da murnar sauyin nan a bangaren ilmi, amma a dalilin yara manyan gobe wadanda za su sami damar su yi wa al’ummarsu ayyukan alheri wata rana da kuma ganin ya bar wani abin da za a rika tunawa da mutumin da aka fi sani ko kiransa da Mutawallen Sakkwato.

  DOKAR TA-BACI

  Bayan ya kama aiki a ofishinsa gadan-gadan, da yake shi mutum ne mai tunani na kwarai ga kuma dimbin kwarewar shugabanci, Tambuwal ya natsu ya kuma dauki lokacinsa sosai don ya bi daki-daki ya karanci dukkan kididdigar da suka shafi bangaren ilmi na jihar. Da zuciyarsa ta kasa amincewa da bayanan da ya samu, sai Gwamnan ya sanya dokar ta-baci a sashen ilmi na jihar. Kafa wannan dokar na nuni da cewa, lallai gwamnati ta fahimci hanyoyin bi da za ta shafe matsalar sarai, kenan ba za ta ci gaba da zama makauniya ba. Gwamnan ya yi wannan sanarwa ne a taron majalisar zartaswa na jiha da suka yi a watan Disambar 2015.

  Kwamishinan kudi na jihar, Alhaji Sa’idu Umar cewa ya yi, ‘’Manufarmu ita ce mu ga mun kara daukar dalibai a dukkan matakai – tun daga mafarin farko zuwa sakandare da ma gaba da sakandare. A karshen wannan tsarin za mu tabbatar duka gurabenmu mun cike su a makarantun tarayyar Najeriya’’.

  Kwamishina Umar ya ci gaba da cewa, ‘’Muna sa ran za mu samar da nagartattun malamai ta hanyar ba su horaswa a kai- a kai da kuma daukar sababbi. Duk malamin da kwazonsa bai yi gaba ba bayan an horas da shi, za a canza masa aiki zuwa inda kwanyarsa ta fi dacewa. Burinmu dai shi ne mu daukaka kwazon mutane a wannan sashe, mu kawar da rashin kwarewa, kuma mu tabbatar da bin ka’ida da yakar jahilci’’.

  Akwai batutuwan da suka dace a ji su daga bakin gwamnati mai gaskiya cikin al’amarinta, wadda da gaske ta fahimci wajabcin sanya jari a bangaren ilmi. Sanya dokar ta-baci a sashen ilmi ya fito da sabon faifai na cewar, gwamnati a shirye take ta tsayar da ingiza kudadenta da sunan tallafa wa ilmi ga wasu masu fadi babu cikawa.

  DOKOKIN BI

  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shi ne ya kirkiro da kudurin dokar ‘yanci ga ilmi ta shekarar 2016, domin ya bai wa yara kariya da kuma ‘yancinsu ga ilmi daga ‘yan shekaru shida ( 6 ) zuwa sha takwas ( 18 ) a Jihar ta Sakkwato. Wannan ne na farko da wata jiha a Najeriya ta yi yunkurin ganin kafa doka don ilmi ya zama ‘yancin dukan yara. Kudurin dokar yana daya daga cikin tsarin dokar ta-baci a bangaren ilmi na jihar wanda aka gabatar a Disambar shekarar 2015.

  Majalisar dokokin Jihar Sakkwato a watan Afrilun shekarar 2017 ta daddale tare da tabbatar da kudurin ya zama doka kan ‘yanci na ilmi kuma kyauta da wajabta ilmin farko ga dukkan yara na jihar. Mai girma Gwamnan ya yi batutuwa biyu masu muhimmanci bayan an kafa dokar inda ya ce, ‘’Wannan shi ne dalilin da ya sanya muka shiga cikin al’amarin gadan-gadan domin yunkurinmu na fadada samar da hanyoyin ilmi a jihar tamu. Shawarar a kafa dokar nan ta haskaka mana bin tafarkin da ya dace na doka, domin sanya dokar ta-bacin nan da muka yi wa sashen ilmin fiye da shekara guda kenan’’.

  ‘’ A matsayin jiha ta farko a Najeriya da muka sanya ilmi ya zama ‘yancin doka, muna sa ran za mu gudanar da sassan na shari’a nan gaba kadan. A wajenmu tabbatar da nasarorinmu a bangaren ilmi yanzu aka fara shi. Muna neman goyon bayan al’ummominmu da masu ruwa da tsaki a harkar ilmi daga nan gida Najeriya da ma kasashen waje domin ya zamanto mun sami damar bai wa ‘ya’yanmu nagartacce kuma samammen ilmi’’. Inji Gwamnan daga bakinsa kai tsaye.

  KASAFI

  Bangaren Majalisar Dinkin Duniya mai kulawa da ilmi, wato UNESCO ta fitar da tsarin kasafin kudaden da suka dace kasashe su bi don ya zamanto masu tsani na kulawa da bangaren na ilmi sosai, saboda yawan bukatuwar da ake da ita na habbaka ilmi, inda suka yanke cewa, kashi 26% cikin 100% na kasafin kudi na kowane wuri ya wadatar.

  Lalacewar da ilmi ya yi kuma domin ya nusar da al’umma yadda gwamnatinsa ta mayar da hankalinta don gyara sashen, Gwamnan ya ware kudade wuri na gugar wuri har Naira Biliyan 29.9 a kasafin kudi na shekarar 2016 ga batun ilmi, kasafin da ya dara kowane bangare na gwamnatin. Kasafin na wakiltar kashi 29% cikin 100% na jimlar kasafin kudin jihar kenan. A shekarar 2017, kasafin kudin a wannan bangare karuwa ya yi, inda aka sami Naira Biliyan 38.4 wanda ke wakiltar kashi 27.3% cikin kashi 100%. Abin ban sha’awa kuma a kasafin kudi na shekarar 2018, bangaren na ilmi ya ci nasarar karuwa inda ya sami Naira Biliyan 57.4, wato kashi 26.1% na kudaden da jihar ke samu daga asusun gwamnatin tarayya.

  Dukkan wadannan kasafin kudade da aka yi, sun zarce tsarin kasafin da UNESCO ta gabatar, kuma wannan ya nuna a zahiri mulkin na Aminu Tambuwal ya gano cewa, hanyar da ya bi na zuba makudan kudade a bangaren na ilmi ta amfanar, kuma wajibi ne ga karko da karfafa zuciya ta dan Adam da kuma ciyar da Jihar Sakkwato gaba.

  DAUKAR ‘YAN MAKARANTA

  Kamar yadda shirin nan a kan tsari da dabarun samar da ilmi na jiha ( SESP ) 2011-2020 a karkashin  ma’aikatar ilmi na shekarar 2010, rahoton ma’aikatar a kan wannan shirin ya nuna cewa, a jihar Sakkwato yawan daukar yara makaranta shi ne kashi 71% da 55.5% a tsakankanin yara ‘yan firamare. Sai dai kuma kididdigar yawan masu zuwa makaranta a shekarar karatu ta 2009-2010 shi ne 68%, sai kuma wadanda suka kammala da batun tazarar jinsi yana da kashi 40%. Wato dai kashi 44.5% na yara masu kanann shekaru ba su sami shiga makaranta ba a shekarar karatu ta 2010. Rahoton ya bayyana yawan yara maza da suka sami shiga shi ne kashi 69.8%, mata kuma kashi 30.2% idan aka kwatanta da yadda aka ba da gwargwadon yawan da ake son a samu na kasa baki daya, wato kashi 86% ga yara maza, kashi 75% ga yara mata.

  Shiri da tsarin daukar dalibai a shekarar 2016/2017, ajiyayyun shaidu sun nuna cewar, an sami ragewar yara ainun da ba sa samun shiga makaranta, an sami kari na kashi 7.3% a shiga ajin gwaji na ‘yan yara, wato fagen sharer shiga firamare, da kuma yaran firamare, kuma daga cikin wannan lissafi, kashi 4.4% yara ne mata.

  A watan Nuwambar 2017, Aminu Tambuwal ya kaddamar da  fadadadden kamfe a Jihar Sakkwato na sanya yara makarantar firamare a shekara mai zuwa, kuma yaran nan kada yawansu ya gaza Miliyan daya da Dubu dari hudu.

  Baya ga wannan kamfe, gwamnatinsa ta bayar da tallafi ga iyayen yara marasa karfin aljihu domin ta goya masu baya wajen sanyawa da kulawa da ‘ya’yansu a makaranta, musamman ma ‘ya’ya mata a yayin da suke cikin karatunsu.

  Shirin daukar ‘yan makarantar ya sami nasara da kyau domin a watan Oktoba, 2017, Jami’in UNICEF na Sakkwato ( kafin a canza masa wajen aiki ), Malam Muhammad Muhuyiddeen ya fadi cewa, an sami ragowa matuka fiye da kashi 50% cikin 100% ga yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Sakkwato. Ya ce, shi a saninsa yawan yaran da ba sa shiga makaranta a Sakkwato, ya janyo ta zama ta butal, wato ta baya, inda ta dare bisa teburin kidaya na kasar nan kan wannan batu,to, amma sai ga shi yanzu ya sauka daga kashi 69% a 2015 zuwa kashi 37% a shekarar 2017.

  ‘’Shirin bincike na MICS na shekarar 2016 zuwa 2017 ya nuna cewa, Jihar Sakkwato ta sami ci gaba na abin a yaba mata, inda sakamakon binciken ya nuna an yanke kashi 50% na yawan yaran da ba su a cikin makaranta. Wannan ya faranta mani zuciya, ganin yadda Jagoran shugabancin na siyasa tare da wasu masana a fannin masu dafa masa baya wadanda gwamnatin ta kafa su yi aiki a UNICEF da ma sauran masu tallafa wa yara a sauran sassan na jihar suka yi namijin kokarin nan’’. Inji Muhammad Muhuyideen.

  DAUKAR AIKI DA BAI WA MALAMAI HORASWA

  Binciken SESP na shekarar 2010 ya bayyana daidaito na malami daya tilo da yara dalibai a Sakkwato shi ne 1:47, wato malami daya da dalibai 47, wanda shi wannan har ya fi kyawo da daidaiton da ake ciki a yanzu na malami daya da dalibai 66, ( 1:66 ). Kai abin ya fi tsanani ma a ce , kwararren malami daidaitonsa da dalibai 144 (1:144 ).

  Ganin haka ne ya sanya Gwamna Tambuwal ya ba da izinin daukar malamai 500 wadanda UNICEF ta bai wa horaswa domin habbaka malaman na makarantun sakandare. Tambuwal ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta dauki kwararrun malamai har su Dubu 10, domin ya zama an fara biyayya ga rahoton da kwamiti kan batun ilmi ya bai wa gwamnati shawarar a yi.

  A watan Mayu 2017 gwamnatin jiha ta ce, an tantance malamai 96 an dauke su a makarantu 10 da suke karkashin kulawar ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Jihar Sakkwato.

  Haka kuma karamin kwamiti a kan dokar ta-baci da gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa, ya bayyana cewa, kashi 31% na malaman makarantun gwamnati  ba su da kwarewa amma ana iya ba su horaswa, kuma su dace kwarai.

  Dalilin wancan batun ne, tuni a farkon wannan shekarar malaman firamare na Jihar Sakkwato har su 3,374 suka fara karbar horaswarsu mai gwabi domin su kara ilminsu da kuma saba wa kawunansu yin aiki da na’urori da kayayyakin zamani na ilmi.

  ILMIN DIYA ( ‘YA ) MACE

  Arewacin Najeriya tun da jimawa shi ne yankin da yake koma-baya a batun ilmin diya mace, niyya da zimmar ganin an yi yunkurin samar da hanyoyin da diya mace za ta sami ilmi a Jihar Sakkwato, gwamnatin jihar ta bayyana kafa Hukumar Ilmin ‘Ya Mace a shekarar 2016. Sabuwar hukumar ke da alhakin tafiyar da dukkan al’amuran da suka shafi ilmin diya mace tun daga farkon karatu har zuwa kololuwarsa.

  Haka kuma gwamnatin jihar ta bullo da tallafi ga ilmin mata, inda take bai wa iyaye mata na karkara wasu kudade domin su kyale ‘ya’yansu mata su shiga makaranta a maimakon tallace-tallace na bisa tituna da suke famar yi. Hakan ya taimaka kwarai na samun yawan ‘ya’ya mata da suka shiga makaranta a jihar.

  SAMAR DA KAYAYYAKI DA GINE-GINE A MAKARANTU

  Juyin-juya hali da Gwamna Tambuwal ya yi a bangaren ilmi ba zai kammalu ba, ba tare da an ambaci kayayyakin da ya samar da gine-ginen azuzuwa da sake fasali ko gyara kacokan kan wasu gine-ginen da suka lalace kuma aka yi watsi da su ba da sauransu.

  Ba zai zama riga malam masallaci ba idan aka ce kimanin makarantu 100 suna ta gudanar da ayyukansu a jihar tun shekarar 2015 har zuwa yau din nan. Makarantun sun hada da sabbin makarantun sakandare ta Arabiyya guda 3 a Illela da Maruda da Dagawa. Sai kananan makarantun sakandare guda 69, a wadannan wurare kamar haka:-

  Gande, Hamma Ali, Mabera, Kaffe, Gumbi, Minannata, Turba, Kalmalo, Araba, Rimawa, Kilgori, Unguwar lalle, Horo, Sanyinnalawal, Bakabe, Arume, Lajinge, Dan Tudu, Labau, Kwakwazo, Lanjegu, Marakawa, Sangarewa, Balle, Chacho, Alkammu, Mujaya, Rabah, More, Lambara, Sabon Garin Dole, Jamali, Kurdulla, Bankanu, Tundun Yola, Kasarawa, ‘Yar Abba, Kauran Kimba, Gidan Bubu, Rikina, Kwannawa, Girkau.

  Gwamnan jihar har ila yau ya raba littattafai na karatu guda Dubu Arba’in da biyar ( 45,000 ) ga sababbin makarantu guda 38 a fannonin karatu daban-daban da suka hada da English Language ( Ingilishi/ Turanci ) da Mathematics ( Lissafi ) da Basic Scienne & Technology            ( Kimiyya da Fasaha ) da Pre- Vocational ( Sana’o’in hannu ) da Islamic Studies ( Darasin Koyon Addinin Musulunci ). Haka Gwamnan ya hada kai da masu ruwa da tsaki a fannin ilmi na kasashen waje kamar USAID ta Amurka, kuma ya tabbatar tare da ganin an rarraba littattafan karatu fiye da Dubu dari biyar ( 500,000 ) ga makarantu sama da 1000 da suke a ffadin jihar tun shekarar 2015.

  Gwamna Tambuwal har ila yau ya raba sababbin motoci kirar Bas-Bas guda 50 ga wasu makarantu a cikin shirin nan na raba motoci ga makarantu, rabon motocin  na farko da aka fara yi. An kebe makarantu 300 ne wadanda za su ci gajiyar wannan shiri na bada motocin makaranta.

  Wasu ayyukan da aka yi watsi da su na makarantu wadanda wannan gwamnati ta ci gadonsu tuni an kammala  ayyukansu, wadannan ayyukan sun hada da , SMSS Illela,  MAASS Maruda, GGSS Gumbi, Model Tudun Wada.

  A shekarar 2015/2016, gwamnati ta raba tebura da kujeru a makarantu har guda Dubu 30,186, sannan a shekarar 2017 ta kara raba guda Dubu 15,740.

  Tambuwal ya gina makarantar GSS Balle da ke karamar hukumar Gudu. Kafin wannan hangen nesa da tsayin-daka na Gwamnan kan ginin makarantar, Gudu ita ce karamar hukuma daya rak da ba ta da Babbar makarantar sakandare.

  BIYAN ALBASHI DA HAKKOKA

  A watan Yuni 2016 ne Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanar cewa, gwamnatin jiha na kashe Naira Miliyan 850 a kan albashin malaman makarantu na wata-wata, wannan ya nuna hoton adalcin gwamnatinsa a fili. Daga shekarar 2015 zuwa yau babu wani tsaiko kan rashin biyan albashin malamai domin karfafa masu gwiwa kan aikinsu. Abin alfahari ba a taba bin Gwamnan bashin albashi ba, idan aka kwatanta hakan da al’amuran da suke faruwa a wasu jihohin kasar nan inda ake kin biyan malaman makaranta hakkokinsu na albashin wata-wata.

  Gwamnatin jiha a yanzu haka ta fara gina gidaje na musamman da ta bai wa sunan ‘Kauyen Malamai’ a shiyyoyin Hakimai daban-daban na jihar. Haka ma kuma a watan na Yuni 2017, Gwamnan ya amince da biyan giratuti na malamai 200 wadanda ka’idar shekarunsu na ritaya ya cika suka ajiye aikinsu da kansu. Kuma ya amince da a fitar da kudi har Naira Miliyan 680 domin a biya masu Fensho daga cikin malamai da ma’aikatan kananan hukumomi. Wannan kari ne ga yadda ya bullo da a rika biyan wasu kudi na musamman tare da kyautata wa malaman da aka tura su yankunan Karkara, domin a kara ba su kwarin gwiwar su ci gaba da ciyar da batun ilmi Jihar Sakkwato gaba.

  TALLAFIN KARATU

  Bayan ya shiga ofis dinsa a shekarar 2015, Aminu Tambuwal ya bayar da umurnin a yi hanzari a biya asalin ‘ya’yan jihar nan da suke karatu a wurare daban-daban a nan gida Najeriya da Kasashen ketare. Tun da asubar fari aka fahimci yana da kyakkyawar niyya ta alheri game da ilmi.

  Sa’ar da wani matashi mai suna Aliyu ya samu, yaro da Allah Ya ba baiwar kere-keren mota, tagomashin Gwamna ya fado kansa, inda Tambuwal ya ba shi Tallain Karatu Na Musamman a wata Jami’a da ke kasar Amurka, domin ya karanto ilmin kere-keren motoci.

  A watan Mayu 2017, Gwamna Tambuwal  ya amince a fitar da kudi har Naira Miliyan 213 don a biya daliban Jihar Sakkwato da suke karatu a kasar Uganda da Sudan da Jamhuriyar Nijar. Ga yadda kasafin rabon kudaden ya kasance:-

  An ware wa daliban Jihar Sakkwato masu karatu a Sudan Naira Miliyan 164,400.

  Daliban kasar Uganda ‘yan asalin Jihar Sakkwato, an ware masu Miliyan 26, 840.

  Daliban Sakkwato masu karatu a Jamhuriyyar Nijar an ware masu Naira Miliyan 22, 676,700.

  Ya zuwa yanzu gwamnati ta biya fiye da Naira Biliyan biyu da rabi ( # 2.5 B ) na tallafin karatu daga watan Mayu na 2015.

  A karshe, tun da mun zama ganau da jiyau kan Juyin-juya hali kan ilmi a Jihar Sakkwato, ya dace mu karfafa wa sauran Gwamnonin Arewa gwiwarsu da ita kanta gwamnatin tarayyar  Najeriya da su kwaikwayi wasu daga cikin tsare-tsaren da suka kawo wa Jihar Sakkwato nasara cikakkiya a wannan juyin-juya hali a kan bangaren ilmi.

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here