‘YAN MAJALISAR DOKOKIN KADUNA DA AKA ZABO DAGA MAZABAR SAMINAKA SUN GAZA-RABI’U  SALISU

0
848

Isah Ahmed Daga Jos

WANI dan takarar kujerar majalisar dokoki ta jihar Kaduna, daga mazabar Saminaka da ke karamar hukumar Lere, karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Rabi’u Salisu Saminaka  ya bayyana cewa wakilan da aka zabo a baya, don su wakilci al’ummar mazabar Saminaka a majalisar dokoki ta jihar Kaduna, sun gaza. Alhaji Rabi’u Salisu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce gazawar da yake ganin wadanda aka zaba a wannan mazaba zuwa majalisar dokoki ta jihar Kaduna  suka yi, shi ne  basu yiwa al’ummar wannan mazaba cikakken wakilci ba.

‘’A gaskiya wadanda aka zaba a wannan mazaba sun yi sakaci wajen rike ‘yan siyasa da al’ummar wannan mazaba gabaki daya. Basu tsayawa su yi mu’amula da al’ummar wannan mazaba, kamar yadda ya kamata. Ya dace duk wanda aka zaba ya wakilcin jama’a ya rika tsayawa yana sauraronsu, yana yi masu bayani kan halin da gwamnati take ciki. Amma abin takaici wakilan da aka zaba a wannan mazaba, basa ta al’ummar da suka zabe su, sai dai ta kansu kawai suke yi’’.

Alhaji Rabi’u Salisu ya yi bayanin cewa wannan ne ya karfafa masa  gwiwar fitowa wannan takara, domin  baiwa al’ummar wannan mazaba wakilci nagari, ta hanyar mu’amula da su tare da yi masu ayyuka daidai gwargwado da kuma kwato masu hakkokinsu.

Ya ce babban abin da zai fi mayar da hankali a kai, idan Allah yasa ya sami nasara shi ne bunkasa ilmi.

Ya ce domin a yanzu babu manyan makarantun  gaba da sakandire a wannan yanki. Don haka karatun gaba da sakandire yana yiwa al’ummar wannan mazaba wuya, saboda matsalar rayuwa da ake fama da shi.  Ya ce  idan Allah yasa ya sami nasara, zan yi iyakar kokarinsa wajen ganin an wadata manyan makarantu wannan yanki.

Har’ila yau ya ce zai tsaya wajen ganin an  bunqasa aikin noma, musamman ganin sunan da  yankin ya yi a duniya, kan aikin noma.

Daga nan sai ya yi  kira ga al’ummar wannan mazaba, su zabi wadanda suka cancanta a zabubbuka masu zuwa, na shekara ta 2019.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here