Za Mu Hukunta Masu Haddasa Rikici A Kaduna – El- Rufa\’i

0
719
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa\'i na Jihar Kaduna

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta sha  alwashin za ta sanya kafar wando daya da masu haddasa tashin hankali a wasu yankunan jihar musamman Kudanci.
Gwamnati ta yi wannan kalaminne  bayan hatsaniyar da ta tashi a garin Kasuwar Magani a
karamar hukumar Kajuru, inda aka kona gidajen mutane da hallaka wasu da dama.
Ba wannan ne karon farko da ake samun rikici mai nasaba da addini da kabilanci a jihar Kaduna ba, kuma gwamnati ta sha shan alwashin magance matsalar.
Amma har yanzu ba ta sauya zane ba. Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya zargi wasu \’yan siyasar yankin da rura wutar rikicin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here