EFCC TA KARBI $375,000 DA JAMI\’AN KWASTAN SUKA KWACE A GARIN KADUNA

0
630
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki
Daga Usman Nasidi
JAMI\’AN rundunar hana fasa-kwauri ta kasa wato kwastan ta mika wa hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wat EFCC zunzurutun kudi har Dalar Amurka dubu 375 da suka kwace daga hannun wani mai suna Adamu Rabi\’u Muhammad a jiya Talata, 6 ga watan Maris, 2018.
Shi dai Adamu Rabiu da ke zaman wani hamshakin dan kasuwa a garin Kano kamar yadda muka samu rundunar jami\’an kwastan din ce ta shiyyar Kaduna suka damke shi a filin jirgin sama na kasa-da-kasa da ke a garin na Kaduna.
Majiyarmu ta samu cewa shugaban hukumar ta EFCC da yake jawabinsa ya gode wa rundunar jami\’an kwastam din bisa namijin kokarin da suke yi wajen ganin sun taimaka masu don gudanar da aikin su.
A wani labarin kuma, Wani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin kasar Najeriya ne da aka haifa a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya da ke tarayyar turai a zaben da ya gudana.
Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami\’in \’yan kasar waje na jam\’iyyarsa.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here