Gwamnatin Jihar Katsina Ta Yi Biris Da Batun Yajin Aikin Da Ma\’aikatan Lafiya Ke Shirin Shiga

0
779

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR Ma’aikatan asibioci na jihar katsina  sun nuna koken su ga Gwamna Aminu Bello Masari saboda kin biyan wasu daga cikin yan’yan kungiyar kudaden albashi da suke bi na tsawan wata 8 zuwa 16.
A lokacin da yake magana da manema labarai, shugaban kungiyar ta jihar, Kwamarad Hussaini Hamisu ya bayyana cewa kimanin yan’yan kungiyar 8450 a dukkanin kananan hukumomin da ke Jihar ta Katsina, lamarin ya shafa.
Kwamarad Hussain ya ce kungiyar na bukatar a biya yan’yan kungiyar hakkokinsu da gaggawa, domin rashin zai iya hadda koma-da-baya a bangaren kiwon lafiya wanda ka iya shafar illahirin bangaren kiyon lafiya a jihar.
Ya kara da cewa, gwamna ne da kansa yayi alkawalin biyan su dukkanin hakkokin su, a lokacin wani taron da kungiyar ta yi tare da kwamitin tantance ma’aitan a watan Yuni  na
2016. Yace tun lokacin da kwamitin tantamcewar ya mika ruhotan aikin da aka sa shi ga gwamnati, har zuwa yau, ba wani memba na kungiyar da aka biya. “kungiyar ta yi zaton tuni kafin kawo yanzu, duk an biya membobin hakkokinsu”. Ya kara da cewa: “membobin kungiyar suna cikin wani irin mawuyacin halin kaka-ni-ka-yi saboda kin biyan hakkokin nasu, Ina kira da asaki kudaden don ba ma’aikatan kwarin gwiywar ci gaba da jajircewa wajen aiki tukuru a bangarorin ayyukan su a fannin kiwon lafiya. Ya kara da cewa “Ma’aikatan lafiya
suna aiki tukuru don ganin sun mai da bangaren lafiyar ya habbaka, don haka biyanmu basuskanmu, shi zai sa mu jajirce wajen ceton rayukan jama’a”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here