JAMI\’AR AHMADU BELLO TA YI WATSI DA YAJIN AIKIN KUNGIYAR MA\’AIKATAN JAMI\’AR

0
553
Daga Usman Nasidi
KUNGIYAR ma\’aikatan jami\’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun bayyana cewar sun janye yajin aikin da suka shiga watanni uku da suka wuce.
Shugaban kungiyar reshen jami\’ar, Abdulrauf Bello, ya sanar da hakan bayan kammala taron kungiyar reshen jami\’ar.
Ma\’aikatan jami\’ar ABU sun janye yajin aiki
\” Ina umarta dukkan \’ya\’yan kungiyarmu da su gaggauta komawa bakin aiki. Tsawon watanni uku kenan muna yajin aiki amma aikin jami\’a bai tsaya ba. Saboda haka yajin aikin ba shi da wani amfani, \” a cewar Abdulrauf.
Sai dai wannan umarni na kungiyar ma\’aikatan jami\’ar ta ABU ta kawo rudani da rabuwar kawuna a tsakanin \’ya\’yan kungiyar domin jim kadan bayan sanarwar janye yajin aikin.
Malam Alfa Gimba, tsohon shugaban kungiyar ma\’aikatan reshen jam\’iar ya fito yana mai bayyana cewar Abdulrauf ba shi da ikon bayar da sanarwar janye yajin aikin domin ba mamba ba ne a kungiyar.
Gimba ya kara da cewar tuni kungiyar ta tsige shi daga shugabancin kungiyar kuma hatta kotu ta ki ta yarda da bukatar mayar da shi, a saboda haka ba shi da ikon bayar da sanarwar janye yajin aikin.
Wasu dalibai da jaridar Daily Trust ta yi hira da su sun bayyana jin dadinsu bisa janye yajin aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here