MALAMAI YA KAMACI SU JAGORANCI RIKICIN YAKI DA BOKO HARAM A SAMBISA – Inji Sheikh Gumi

0
693
Daga Usman Nasidi
SHAHARARREN malamin addinin Musulunci da ke garin Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya shawarci Hukumar Sojin Najeriya ta kirkiri rundunar musulmi na musamman da za ta yaki Boko Haram
Ya ce rundunar da za a kirkira za ta yi amfani da ka\’idoji da dabaru irin na addinin Islama wajen yaki da Boko Haram
Babban Malamin ya ce ba za  a iya cin galaba kan Boko Haram ba har sai an bi ka\’idojin yaki irin na addinin musulunci.
Sheikh Gumi, ya yi kira da a ba wa Malamai dama a bangaren Sojojin Najeriya don taimakawa wurin yakar \’yan Boko Haram bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Sheikh Gumi ya kara da cewa, kowane bangaren na yakin zai zama karkashin jagorancin Malamin Addini, ya ce ba za a taba cin nasara a yaki da ‘yan kungiyar ba idan har ba ka’idojin addinin musulunci aka yi amfani da su ba.
Malamin ya ce \”wasu daga cikin matakan Jami’an namu suna shiga cikin rudani, shi ya sa duk sa\’adda ‘Yan kungiyar ta Boko Haram suka fadi Allahu Akbar (Allah mai girma), wasu daga cikin Sojojin namu sai ka ga sun watsar da makaman nasu sun zuba a guje. Amma idan muna da musulmai a karkashin jagorancin Malamai, za su yi yaki ne a matsayin Jihadi.
\’\’Ina ganin idan muka jaraba wannan shawarar zai kawo karshen tashin hankula. Abin yana bani mamaki, saboda haka dole mu yi amfani da ka’idoji na Addini wurin wannan yakin\’\’.
Shaikh Gumi ya kuma ce, musulmai ne kadai za su iya yakar Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya, har ma a duniya baki daya.
Mashahurin Sheikh din ya ce akwai bukatar kungiya tsakanin Musulmai da sauran Addinai don kawo karshen wannan ta’addanci.

 


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here