An Kashe Gawurtaccen Dan Fashi Buharin Dajin Da Ya Addabi Zamfara

0
1930

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Buharin Daji jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da hare-hare.
Wani babban Jami\’an gwamnatin jihar ya shaida wa manema labarai cewa jami\’an tsaro sun mika wa mahukunta gawar madugun \’yan fashin.
Masu satar shanun dai sun kwashe shekaru suna kisan rayuka da satar shanu a jihar.
Bayanai sun nuna cewa ranar Laraba ne aka kashe Buhari Tsoho, wanda aka fi sani da
Janaral Buharin Daji a wani farmaki da aka kai masa da taimakon wasu abokan fashinsa da
suka raba gari.
Alhaji Sani Ahmed Gwamna, wakili a kwamitin wanzar da tsaro na jihar ya ce an mika gawarsa ne ranar Juma\’a da maraice a fadar gwamnatin jihar.
Sama da mutane dubu daya suka rasa rayukansu a cikin hare-haren \’yan fashin a jihar cikin shekaru bakwai.
Kuma jihar Zamfara na cikin jihohin  da ke fama da matsalar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.
Gwamnatin jihar Zamfara ta taba kulla yarjejeniya da Buharin Daji a watan Fabrairun 2017 domin samun zaman lafiya a jihar.
Amma kuma babu wani sauki da aka samu a matsalar ta kashe-kashen mutane a sassan jihar. Ko makwannin baya \’yan bindiga sun kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.
Dan majalisar dattawan da ke wakiltar Zamfara Sanata Kabiru Marafa, a watan jiya ya shaida wa manema labarai cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a sassan jihar cikin shekara biyar.
Akwai rundunar Soji ta Operation harbin kunama da aka kaddamar a Zamfara domin yaki da barayin shanu da \’yan fashi, amma duk da haka ana ci gaba da kashe mutane.
Masu sharhi kan sha\’anin tsaro da ma \’yan kasar na ganin matakan da ake dauka ba su yi tasirin hana kai hare-haren ba a Jihar.
Yanzu dai ba a sani ko mutuwar Buharin Dajin zai sa a samu dauwamammen zaman lafiya a Zamfara koko a\’a akwai sauran burbushin yaransa ko abokanan barnarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here