Buhari Ya Je Jahar Filato domin Kaddamar Da Ayyuka Da Jaddada Zaman Lafiya

0
579
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA Muhammadu Buhari ya isa jahar Filato a ci gaba da kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar nan da kuma kaddamar da ayyukan ci gaba.
A ci gaba da ziyarce-ziyarcen jajantawa da na kaddama da ayyuka da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi, ya ziyarci jahar Filato  inda ya sauka filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke Haifang daura da Jos, babban birnin jahar Filato da misalign karfe 12 na rana
inda jama’a da dama daga sassa daban- daban da kuma jam’iyyu daban-daban suka fito domin marabtar Shugaban.
Shugaba Buhari ya kaddamar da ayyukan da su ka hada da hanyar Mararrabar Jama’a wadda ke hada Abuja da Filato da kuma sauran jahohin Najeriya. Buhari ya kuma kai
ziyara Fadar Sarkin Jos (Gbong Gom Jos) inda suka kebance cikin Fadar ba tare da ‘yan jarida ba.
Daga cikim abubuwan da Buhari ya je yi a Filato har da ganawa da masu ruwa da tsaki na bangarori daban- daban a jahar da zummar tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabanbantan al’ummomi. A yayin da jama’ar jahar ke yaba ma Buhari kan yaki da
almundahana da ya ke yi a kasar, su na kuma fatan zuwansa zai karfafa zaman
lafiya tsakaninsu. shi ne irin dafifin da jama’a su ka yi cikin birnin Jos don su ga Shugaba Buhuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here